Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
Fulanin Afirka sun karamma Shugaban Miyetti Allah Kautal Hore a Gambiya

Uwargidan Shugaban Qasar Gambiya Fatimata Baro ke miqa lambar yabo ga Alhaji Bello Boxejo

Fulanin Afirka sun karamma Shugaban Miyetti Allah Kautal Hore a Gambiya

Kungiyoyin Fulani daga kasashen Afirka ta Yamma da suka gudanar da taro a birnin Banjul na kasar Gambiya, sun karamma Shugaban Kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore ta Kasa Alhaji Abdullahi Bello Bodejo kan irin shugabanci da yake yi wa al’ummarsa da kare hakkokinsu.

Wata sanarwa da ta fito daga kungiyar ta hannun sakatarenta na kasa Injniya Saleh Alhassan wanda ke cikin ayarin da ya halarci taron, ta ce matar Shugaban Kasar Gambiya Malam Fatumata Baro ce ta mika lambar yabon a madadin mijita Shugaba Adama Baro, wadanda dukkansu Fulani  ne.

Ya ce kungiyar ta Miyetti Allah Kautal Hore ta je taron ne da ya gudana tsawon wuni 3, bayan gayyatar da ta samu kamar sauran takwarorinta na wasu kasashe daga yankin Afirka ta Yamma, inda aka tattauna matsalolin da suke addabar al’ummar Fulani kamar na tarbiyya da watsi da dabi’un Fulani, sai kuma koma baya wajen sa yara a makaranta, kamar yadda bayanin ya nuna. Haka sanarwar ta ce an shirya bukukuwan al’adun gargajiya na Fulani a yayin taron inda mawakan Fulani daga Najeriya irin su Hauwa’u Gombe da Baba Sajo daga kasar Kamaru da Fouta Jaloo daga kasar Guinea suka nishadantar da mahalarta taron ciki har da Turawa da ke aiki a kasar.

Alhassan ya ce a wuni na uku ne Uwargidan Shugaban Kasar, ta shirya liyafar cin abincin dare a Fadar Shugaban Kasa, inda ta mika kyautar girmamawa ta kungiyoyin Fulani a madadin mijinta wanda ba ya kasar a lokacin.