✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

FURE: Labarin Uwargida Farida

Muna sanar da dimbin masu bibiyar shafin nan cewa daga mako mai zuwa za mu dawo da wannan labarin. Za mu fara tsakuro shi daki-daki…

Muna sanar da dimbin masu bibiyar shafin nan cewa daga mako mai zuwa za mu dawo da wannan labarin. Za mu fara tsakuro shi daki-daki har zuwa karshe in Allah Ya yarda. Wannan ya faru ne saboda dimbin sakonnin da muke samu na bukatar a dawo da shi. Domin wadanda ba su san da labarin ba, za mu faro shi tun daga farko.

***

Ga tsakure

Tana gama bayaninta, shi kuma sai ya dauki lokaci yana wani zane-zane a kan wani rairayi fari tas da ke zube a kan wani faifai. Bayan ya kammala sai ya kalli idanuwanta kai-tsaye. “Tashi ki matso nan gabana!”

Saratu ta kidime, tsoro ya kara kamata.

“Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un!”

Kalmomin da ta yi ta maimaitawa ke nan a cikin zuciyarta.

“Ko ba ki jina ne? Na ce tashi ki matso kusa da ni, akwai abubuwan da zan duba ne a jikinki, kafin in san matakin da zan dauka don samar miki da bukatarki.”

Ba ta san lokacin da ta tashi ta matsa kusa da shi ba. Shi kuma ya tashi tsaye, ya kama tafin hannunta, ya duba dukkan yatsunta daya-bayan-daya. Ya sanya hannunsa na dama kan goshinta, ya tsaya haka na dan lokaci. Daga bisani ya koma ya zauna.

“Ki mike kafafunki.”

Ya kama yatsun kafafunta ya dudduba, sannan ya koma kan shimfidarsa ya sake zama. Ya dauko farin yashin nan ya ci gaba da zane-zane. Daga nan ya nisa, ya aje faifan, ya dago kai ya kalle ta cikin ido kai-tsaye.

“Na karanta dukkan matsalolinki kuma tuni na tanadi hanyoyin magance su. Abu guda zan gaya miki, kada ki yi kokwanto kuma kada ki yi gardama ko musu; duk abin da na bukaci ki aikata, ki aikata kawai!”

Ita dai Saratu ta yi kasake tana kallonsa kuma tana jin dukkan abin da yake gaya mata. Daga bisani ya jera mata wasu bayanai tare da wasu bukatu da wasu sharudda. “Ki je ki shirya, nan da jibi ki dawo nan!”