✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Furodusa Ekta ya yi shirin ciyar da mabukata a Indiya

Furodusan fina-finan Indiya, Ekta Kapoor ya kuduri aniyar shirya walimar shan ruwa ga mabukata a duk tsawon watan Ramadan a sassa biyar na unguwannin mabukata…

Fostar fim din Once Upon A Time In MumbaiFurodusan fina-finan Indiya, Ekta Kapoor ya kuduri aniyar shirya walimar shan ruwa ga mabukata a duk tsawon watan Ramadan a sassa biyar na unguwannin mabukata na birnin Mumbai, Indiya.
Furodusan, kamar yadda kafafen watsa labarai suka ruwaito, ya shirya yin haka ne domin karrama Musulmi masu azumi kuma da nufin nuna godiya ga sabon fim dinsa da ya kammala, mai suna ‘Once Upon A Time in Mumbaai.’ Fim din dai yana dauke da zaratan ’yan wasa ne Musulmi, kamar su Akshay Kumar da Imran Khan da Sonakshi Sinha da Sonali Bendre da sauransu. Haka kuma ya shirya fitar da shi kasuwa a ranar 8 ga Agusta, ranar da ake sa ran za ta kasance karamar Sallah.
Kamar yadda Ekta Kapoor ya ce: “Ni mutum ne mai daraja addini. Irin yadda albarka ke zuwa mani a kowane lokaci, shi ya sanya nake kukewa da addu’a kafin a ce na fitar da fim dina kasuwa. Don haka saboda sabon fim dina na ‘Once Upon A Time In Mumbai, wanda yana daya daga cikin manyan fina-finan da ake ji da su a bana, na kuduri aniyar ciyar da buda baki ga mabukata a lokacin azumin Ramadan na bana. Wannan na daya daga cikin hanyoyin neman albarka.”