✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Furodusa Haruna Ar-Rahuz ya kwanta dama

Babban dan kasuwar fina-finai kuma Furodusa, Rabi’u Haruna Ar-Rahuz ya kwanta dama. Jarumin ya rasu ne a Kano a ranar Juma’ar da ta gabata, inda…

Babban dan kasuwar fina-finai kuma Furodusa, Rabi’u Haruna Ar-Rahuz ya kwanta dama.

Jarumin ya rasu ne a Kano a ranar Juma’ar da ta gabata, inda aka yi jana’zarsa a gidansa da ke Danladi Nasidi.

Dan uwan jarumin, Sani Haruna Ar-Rahuz ne ya fara sanar da rasuwar jarumin a shafin sada zumuntansa na Instagram.

Jarumin ya rasu ne bayan ya yi fama da jinya sakamakon hadarin mota da ya yi a ranar 12 ga Fabrairu, 2019 lokacin da yake kan hanyarsa ta dawowa Kano daga Yola.

Marigayin ya rasu ya bar mata daya da ’ya’ya shida, maza uku da mata uku.

Marigayi Rabi’u Haruna Ar-Rahuz
Marigayi Rabi’u Haruna Ar-Rahuz

Marigayin wanda shi ne ManajanDaraktan Kamfanin Shirya Fina-Finai na Ar-Rahuz Film Production ya dauki nauyin shirya fina-finan da suka hada da ‘Matar Mijina’ da ’Yan Nepa’ da ‘Idi Wanzami’ da ’Yar Amana da ‘Takanas Ta Kano’ da sauransu.

Fitacciyar marubuciyar littattafan Hausa da kuma fina-finan Hausa, Fauziyya D. Sulaiman ta bayyana kaduwarta sakamakon rasuwar furodusan.

Ta bayyana hakan ne a shafinta na Facebook, inda ta ce, “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un! La haula walakuwwata illah billah! Tabbas Ar-Rahuz mutum ne nagari, kuma jinyar da ya yi ibada ce, sai dai mun yi babban rashin da ba za a mayar da shi ba. Allah Ya ba iyalinsa dangana, dan uwansa Sani kuma Allah Ya ba shi ladan zumunci, domin yana ta kokarin ganin yadda za a fita da shi waje domin samun lafiyarsa, amma Allah Ya fi mu kaunarsa, Allah Ya sa can ta fi nan, amin.”