✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fuskoki da bayanan Musulmin da aka kashe a masallatan New Zealand

A ranar Juma’ar da ta gabata ce duniya ta haku da wani mugun labari, bayan da wani kan ta’adda kan asalin kasar Austireliya mai suna…

A ranar Juma’ar da ta gabata ce duniya ta haku da wani mugun labari, bayan da wani kan ta’adda kan asalin kasar Austireliya mai suna Brenton Tarrant ya auka wa masallatai biyu ya buke wuta a kan masallata a daidai lokacin da suke Sallar Juma’a, inda ya kashe Musulmi 49.

Kan ta’addan mai shekara 28 ana zargin mai akidar fifita fararen fata ne a kan sauran al’ummar duniya.

Jaridar New Zealand Herald ta buga hoton wakansu daga cikin Musulmin da aka kashe, wakanda ta bayyana su da iyaye maza da mata da kakanni da ’ya’ya maza da mata da suke zaman gudun hijira da wakanda suka yi kaura zuwa kasar New Zealand da ma wakanda aka haife su a can. Kuma dukansu ana kaukarsu ne a matsayin ’yan kasar New Zealand.

Ga sunan wakanda aka kashe ko suka bace bayan wannan mugun hari na ta’addanci a garin Christchurch da ke kasar ta New Zealand:

Mucad Ibrahim, shekara 3: Yaro kan shekara uku, Mucad Ibrahim ana jin shi ne mafi karancin shekaru cikin wakanda aka kashe a harin. Yaron sun tafi Masallacin Al Noor ne tare da mahaifinsa da kan uwansa Abdi inda harin ya rutsa da su.

Mucad ya rasu a cikin turmutsitsi bayan da maharin ya fara buke wuta, yayin da Abdi ya gudu, mahaifinsu kuma ya kwanta kamar ya mutu bayan an harbe shi. Iyalansa sun yi ta neman yaron a asibitin Christchurch ba tare da sun gano shi ba, daga bayan sun sanya hoton Mucad, yana murmushi tare da Abdi, hake da kalmar “Daga Allah muke kuma gare Shi za mu koma. Mun yi rashinka kan uwanmu abin sonmu.”

Zulfirman Syah da kansa Aberroes: Alta Marie ta ce mijinta Zulfirman Syah ya kare kansu lokacin da aka kai hari a Masallacin Linwood. Jarumtar Syah ta jawo masa hakuwa da harsasai da yawa da raunuka masu tsanani fiye da kansu Aberroes, inji ta. Amma ta ce shi ma yana farfakowa bayan samun kula da aikin da aka yi masa, yayin da kansu Aberroes ya samu kananan raunuka da suka haka da harbin bindiga a kafa da bayansa.

“Ina godiya ga Allah, iyalaina suna raye, domin an rasa rayuka da dama a harin. Ku sanya wakannan mutane a tunaninku da addu’o’inku,” inji  Alta Marie wadda ta ce watansu biyu kacal da kaura zuwa garin Christchurch.

Abdullahi Dirie, shekara 4: Abdulrahman Hashi, mai shekara 60, wani mai wa’azi ne a Masallacin Dar Al Hijrah a birnin Minneapolis, a Amurka, ya ce kan ’yar uwansa mai shekara 4 yana cikin wakanda aka kashe. Surukinsa Adnan Ibrahim Dirie wanda yake kwance a asibiti saboda harbin bindiga ya kira shi a waya ya shaida masa haka. Huku daga cikin ’ya’yansa sun tsira ba tare da ko kwarzane ba, amma karaminsu Abdullahi an kashe shi. Iyalan sun yi hijira ne daga Somaliya a tsakiyar shekarun 1990.

 Sayyad Milne, shekara 14: Mahaifin Sayyad yana magana cikin hawaye kan “kan karamin sojansa” da ya rasu a harin na Masallacin Al Noor. Mai shekara 10 kuma kalibin makarantar Cashmere High School yana masallacin ne tare da mahaifiyarsa da abokansa masallacin da yake zuwa kowace Juma’a.

Mahaifinsa John Milne ya ce, cikin hawaye “Na rasa kan karamin kana wanda ya cika shekara 14. Amma na dangana.”

Khaled Mustafa da kansa Hamza mai shekara 16: Iyalan Khaled Mustafa sun koma New Zealand ne don samun mafaka daga kashe-kashen da ke aukuwa a kasar Siriya ’yan watannin da suka gabata.

Amma sai ga shi ya haku da fushin mai nuna kiyayya ga Musulmi. An harbe shi a lokacin da yake Sallah tare da ’ya’yansa biyu Hamza wanda ya bace kuma ake tsoron ya rasu da Zaid mai shekara 13 wanda yake farfakowa bayan an yi masa tiyatar rauni ta awa shida a asibitin Christchurch.

Naeem Rashid da kansa Talha mai shekara 21: An bayar da rahoton cewa Naeem ya rasu ne a asibitin Christchurch, bayan ya yi kokarin ya kwace bindiga daga maharin a Masallacin Al Noor. Kansa Tahla ma an bindige shi. Naeem ya fito ne daga Pakistan, inda ya yi aiki a wani banki kafin ya kaura zuwa birnin Christchurch don yin aiki a matsayin malamin makaranta.

Surukinsa Dokta Khursheed Alam ya tabbatar wa kafar labarai ta ARY News cewa su biyun sun rasu a harin.

Farhaj Ahsan, 30: Ashan mai shekara 30, ya bar gidansu da suke zaune tare da matarsa Insha Aziz da ’yarsa mai shekara 3 da kansa mai wata 7 don zuwa Sallar Juma’a.

“Ban san inda kana yake ba,” mahaifinsa Mohammad Sayeeduddin ya shaida wa jaridar Herald daga gidansa a birnin Hyderabad na kasar Indiya.

Ya ce suna magana da matarsa Insha tun faruwar harin, amma yana fata a kawo masa labari mai daki game da kansa. Ashan dai Injiniyan Kwamfuta ne da ya yi digiri na biyu daga Jami’ar Auckland a shekarar 2010 kafin ya koma Christchurch da zama.

Mojammel Hok, shekara 30: Hok, daga Bangladesh, yana cikin mutanen da suka bace kamar yadda wani abokinsa ya shaida wa jaridar Herald. Yana zaune a birnin Christchurch ne tsawon shekara biyu yana kalibta.

Atta Elayyan, shekara 33: Elayyan gola ne a kungiyar kwallon kafa ta Futsal ta kasar da kuma kulob kin maza na Canterbury. An haife shi a Kuwait, kwanan nan matarsa ta haihu kuma sananne ne a masana’antar kere-kere ta garin Christchurch. Shi darakta ne kuma mai hannun jari kamfanin da ake kira LWA Solutions. Kan bindigar ya harbi Elayyan a daidai lokacin da yake Sallah.

Abdelfattah Kasem, mai shekara 59: Shi ne tsohon Sakataren Kungiyar Musulmin birnin, an haife shi a Palaskinu kuma ba a gan shi ba tun lokacin da kan bindigar ya shiga Masallacin Al Noor.

Linda Armstrong, mai shekara 65: Wata kawarta ta ce ta rasu ne a hannun wata mace wadda ita ma aka harbe ta a dantse a Masallacin Linwood amma ta rayu.

Kawaye sun ce koyaushe Armstrong takan kai mutane gidanta kuma tana da kirki. “Koyaushe tana jin dakin ta yi wani abu mai kyau. Tana jin dakin yin haka,” inji su.

Ali Elmadani, mai shekara 66: Wanda aka haifa a Palaskinu, matarsa Nuha Assad ta ce ba ta ji kuriyarsa ba tunda ya tafi Masallacin Al Noor yin Sallah.

Haji-Daoud Nabi, mai shekara 71: Wanda yake jagoranta kungiyar mutanen Afghanistan, yana cikin masallacin a lokacin harin, kuma ana jin ya rasu a ciki.

Kansa Omar Nabi wanda ya je kotu ranar Asabar lokacin da aka gurfanar da wanda ake zargi da kisan kai ya bayyana kisan da “Aikin matsorata.”

Lilik Abdul Hamid: wani ya rubuta a shafinsa na facebook cewa “Abokin gwagwarmaya… ya rasu a New Zealand, ya haku da fushin wani dabba kan ta’addan NZ.”

Ashraf Ali: Wanda ya fito daga kasar Fiji yana daga cikin wakanda suka rasu. Abokinsa Abdul Kayyum ya shaida wa Daily Mai ta Austireliya cewa: “Tare muka yi makaranta. Kuma muna da wasan da muke kira Last Card. Duk lokacin da na gan shi nakan kira shi da Last Card, shi ma in ya gan ni yakan kira ni da Last Card.”

Amjad Hamid, mai shekara 57: Likitan zuciya ne da ya koma New Zealand daga Palaskinu, ba a gan shi ba tun ranar Juma’ar kuma iyalansa suna ganin likitan na Asibitin Hawera ya rasu ne a harin.

Sauran wakanda suka rasu sun haka da Syed Jahandad Ali mai shekara 34 daga Pakistan da Hussain Al-Umari mai shekara 36 daga Hakakkiyar Daular Larabawa da Osama Adnan, mai shekara 37 daga Palaskinu da ya zauna a Masar da Kamel Darwish, mai shekara 39.

, shekara 25: Alibaba, mace mai shekara 25 ta fito ne daga kasar Indiya, kuma tana daga cikin wakanda suka bace bayan harin.

Bora Ramiz, shekara 28: Ramiz yana daga cikin wakanda ba a gani ba. Matarsa Hanan ta ce ita da mijinta sun kaura zuwa birnin Christchurch shekara 23  ne da suka gabata.

Yaro kan shekara 12: Heba Sami, wadda aka harbi mahaifinta aka raunata shi lokacin da yake kare ’ya’yansa ta shaida wa kafar labarai ta Gulf News cewa ta rasa abokan iyalansu biyar ciki har da wani kan shekara 12.

Dokta Haroon Mahmood, mai shekara 40: Yana da mace kaya da ’ya’ya biyu, kuma yana aiki a matsayin mataimakin daraktan harkokin karatu a Kwalejin Canterbury, wata makaranta mai zaman kanta da ke koyar da Ingilisihi  da harkokin kasuwanci.

Husne Ara Parbin, mai shekara 42: Wadda ta yi kokarin ceto mijinta Farid Uddin da ke amfani da keken marasa lafiya saboda shanyewar barayin jiki.

Mohammad Imran Kahn, mai shekara 47: Wanda yake da gidajen cin abinci biyu a birnin Christchurch, ciki har da Indian Grill.

Sauran wakanda suka rasu sun haka da Syed Jahandad Ali mai shekara 34 daga Pakistan da Hussain Al-Umari mai shekara 36 daga Hakakkiyar Daular Larabawa da Osama Adnan, mai shekara 37 daga Palaskinu da ya zauna a Masar da Kamel Darwish, mai shekara 39. Allah Ya jikansu da rahama.