✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fuskokin masu kirgar gero na Yawuri

Lokacin da labarin matasan da suka sa kansu kirga  buhun gero a Yawuri, ya bayyana jama’a da dama sun rika kashe kunne su ji  sakamakon…

Lokacin da labarin matasan da suka sa kansu kirga  buhun gero a Yawuri, ya bayyana jama’a da dama sun rika kashe kunne su ji  sakamakon kirgar don gano adadin da ke cikin buhu mai nauyin kilo 100. Matasan dai manufar su ita ce su san adadin da ke cikin buhun duk da yake sun ce, kirgar geron ba rashin aikin yi ba ne ya sa suke yi.

Hakimin garin Yawuri, Sarkin Yakin Yauri ya bayyana wa Aminiya cewa, mafi yawan masu kirgar masu ayyukan yi ne da suka kammala karatun digiri. Wakilanmu ya ziyarci inda ake kirgar a garin Yawuri don gane wa idanunsa yadda kirgar ke gudana da kuma yadda matasan suke kirgar tare da ba shi muhimmanci.

Suleiman Muhammed Utono malami a Kwalejin Share Fagen Shiga jJmi’a ta Yawuri kuma kwararre a fannin Kimiyyar Kwamfuta a makarantar yana kuma lura da shafin yanar gizo na makarantar, yana daya daga cikin masu kirgar geron saboda alfanun da kirgar ke da shi a garin.

Utono ya ce, lissafi da kirgar na da alaka. Don haka akwai bukatar a inganta al’adar kirga da kuma kara wa jama’a kwarin gwiwa wajen ilimin lissafi.

Daga cikin abin da na fahimta na aikin malanta mafi yawan dalibai na da karancin ilimin kirga. Don haka kirgar kwayoyin miliyoyin gero za ta bunkasa dabi’ar kirga a unguwaninmu. Kirgar za ta taimaka mana sanin miliyoyin lambobi da kuma yadda ake tara lambobin wuri guda. Kirgar gero ta kasance wani abin alfahari a  yau da aka fara daga yin gardama.

Mun amince da fara kirga a maimakon gardamar da ba ta da amfani, hakan ya sa muka fara kirgar don sanin adadin kwayar geron da ke cikin buhu mai nauyin kilo100.

Wannan ya sa kirgar ta zama wata sabuwar fasaha. Na yi bincike a shafukan yanar gizo don sanin ko wadansu sun taba yunkurin kirga buhun gero, amma babu wanda ya taba sai yanzu da mu muka fara yi. Hakan ya sa jama’a da dama daga sassan duniya suke ta kokarin sanin yadda muke gudanar da kirgar gero buhu daya mai nauyin kilo 100. Wannan na nuna duk abin da ake son kirgawa, za a iya mai da hankali a kuma samu nasarar abin da ake bukata.

Muna da yakinin ba abin da zai gagari mutum idan har ya sanya shi a gaba. Abin yabawa ne wannan aikin da muka sanya kanmu a ciki. A yau idon duniya na kanmu. Mutane da dama daga sassan duniya na da sha’awar abin da muke yi kuma sun kosa a sanar da sakamakon kirgar geron. Ina da yakinin cewa, sakamakon kirgar geron.

Akwai yiwuwar cewa sakamakon kirgar geron zai taimaka wa al’ummma. Don haka yana da kyau  duk wahalar abu idan har zai amfani al’umma su aiwatar da shi duk wahalarsa, ina farin cikin zama daya daga cikin masu kirgar gero na Yawuri.

Daya daga cikin masu kirgar Adamu Tasi’u wanda yake likitan hakora ne a Babban Asibitin Yawuri kuma dan kasuwa. Ya ce “Kuma ni ne Mataimakin Manajan Kamfanin A. A Haladu and Brothers Trading Company, na shiga sahun masu kirgar geron ne, saboda na fahimci babu wanda ya taba irin wannan hidimar kirga da muka sanya kanmu na sanin adadin geron da ke cikin buhu mai nauyin kilo 100, wannan zai gamsar da jama’ar karamar hukumarmu da jihar Kebbi. Wannan kirga ta sa aka kara saninmu a duniya kuma jama’a na goyon bayanmu. Kwanan na amsa kiran waya daga China da Malesiya, Adamu Abubakar wanda ke karatu  a Jami’ar China ya kira ni, na yi murnar zama daya daga cikin masu kirgar geron. Muna samun kwarin gwiwa daga wurin Sarkin Yawuri wato Sarkin Yakin Yawuri. Duniya na sauraran sakamakonmu.

Wannan kirga zai zama tarihi saboda su ne na farko da suka fara wannan kirga. Ba wai muna yi ba ne saboda ba mu da aikin yi muna da takardun shaidar digiri da shaidar Ilimi ta Kasa (NCE) da kuma Diploma.

Ahmad Sarkin Yaki wanda yake shi ne Shugaban Kwamitin Kirgar Geron yana da shaidar kammala karatun digiri ya kuma dade yana aikin malanta na tsawon shekara 13. A yanzu haka yana koyarwa a makarantar firamare ta Bioraj Model ta Yawuri yana kuma sana’ar sayar da albasa da kifi.

Daya daga cikin masu kirgar, Lukman Abubakar yana da shaidar digiri a harshen Ingilishi daga Jami’ar Usman Dan Fodiyo da Sakkwato. Kuma yana sana’ar kafinta da dinki.

Sai kuma Buhari Labbo malamin a makarantar  firamaren Nizamiyya Yawuri, ya ce ya kai sama da shekara biyu yana koyarwa kuma har yanzu malami ya kasance daya daga cikin masu kirgar geron na Yawuri.