Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta ce Jam’iyyar APC ta lashe zabe a 13 daga cikin jihohi 20 da ta bayyana sakamakonsu. Jihohin sun hada da Neja da Legas da Gombe da Jigawa da Kebbi da Kwara da Nasarawa da Borno da Yobe da Kaduna da Katsina da Ogun da kuma Zamfara. Jam’iyyar PDP kuma ta lashe jihohi bakwai da suka hada da Abiya da Ebonyi da Akwa Ibom da Kuros Ribas da Oyo da Delta da kuma Enugu. A kasa ga zababbun gwamnonin da jam’iyyunsu
A kasa ga zababbun gwamnonin da jam’iyyunsu:
Jiha Gwamna Jam’iyya
1. Abiya Okezie Ikpeazu PDP
2. Akwa-Ibom Udom Emmanuel PDP
3. Borno Babagana Zulum APC
4. Kuros Riba Benedict Ayade PDP
5. Delta Ifeanyi Okowa PDP
6. Ebonyi Dabid Umahi PDP
7. Enugu Ifeanyi Ugwuanyi PDP
8. Gombe Inuwa Yahaya APC
9. Jigawa Mohammadu Abubakar APC
10. Kaduna Nasir El-Rufai APC
11. Katsina Aminu Masari APC
12. Kebbi Atiku Bagudu APC
13. Kwara Abdulrahman Abdulrazak APC
14. Legas Babajide Sanwo-Olu APC
15. Nasarawa Abdullahi Sule APC
16. Neja Abubakar Bello APC
17. Ogun Dapo Abiodun APC
18. Oyo Seyi Makinde PDP
19. Yobe Mai Mala Buni APC
20. Zamfara Mukhtar Idris APC