✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fyade: Gurmeet Ram Rahim Singh ‘mugun dabba ne’ – Alkali

Alkalin da ya daure shugaban addinin nan na Indiya (Guru) kan laifin fyade, inda ya kira shi da ‘mugun dabba’ da bai cancanci a sassauta…

Alkalin da ya daure shugaban addinin nan na Indiya (Guru) kan laifin fyade, inda ya kira shi da ‘mugun dabba’ da bai cancanci a sassauta masa ba.

Alkalin Jagdeep Singh ya ce cin zarafin da shugaban addinin Gurmeet Ram Rahim Singh ya yi wa mabiyansa “fyaden cin amana ne” kuma ya “cancanci hukunci mai tsanani.”

Kotun ta samu shugaban addinin mai da’awar tsarkaka da laifin yi wa mabiyansa mata biyu fyade a 1999 zuwa shekarar 2002. 

Lauyan matan ya ce, “Mata 40 zuwa 50” sun fito sun yi zargin yi musu fyade kuma za su bukaci a kara bincike a kan lamarin. 

Baya ga tuhumar yin fyade, Ram Rahim Singh ya musanta tuhumar kisan kai biyu da aka shriya za a saurara a wannan wata. 

Mabiyan Ram Rahim Singh sun tayar da bore inda aka kashe mutum 38 bayan da aka same shi da laifi a ranar Juma’a. Kuma an kai alkalin zuwa cikin kurkukun da ake tsare da dan kwalisar shugaban addinin don yanke masa hukunci a ranar Litinin da ta gabata. Alkali Singh ya fadi cikin kakkausar murya cewa, wanda ya yanke wa hukuncin ya cancanci “hukunci mai tsanani” saboda “ya nuna shi mutumin Allah ne amma ya rika amfani da matsayinsa da ikonsa yana tafka ta’asa.” Kamar yadda wakiliyar BBC a Delhi Geeta Pandey ta ruwaito.

“Wadanda aka yi wa fyaden suna daukar mai laifin kamar ‘ubangiji’ kuma suna tsarkake shi. Sai dai kuma mai laifin ya ci mummunar amana ta hanyar yin lalata da wadannan makafin mabiya,” takardar hukuncin ta bayyana.

A matsayin Ram Rahim Singh na “Babban mai fada-a-ji, ya wajaba a daure shi yadda ya kamata domin zama ishara ga masu niyyar aikata haka,’ inji alkalin.

 Ya kara da cewa, “Yanke masa hukunci mai sassauci zai girgiza martabar kasar nan.”

Lauyoyin Ram Rahim Singh sun ce ya kamata kotun ta yi masa hukuncin tsaka-tsaki, saboda “yana fama da cutar hawan jini da ciwon suga da kuma mummunan ciwon baya” kuma a matsayinsa na “wani dan kasa mai bin doka” wanda “yake gudanar da wasu ayyukan inganta rayuwar jama’a” kuma yake gudanar da asibitoci da sauran ayyukan kyautata jin dadin jama’a domin amfanin mutane.

Sai dai a karshe alkalin ya ki amincewa da rokon inda ya ce: “A lokacin da mai laifin ya gaza kyale mabiyansa masu gaskiya kuma ya yi aiki kamar na mugun dabba, bai cancanci samun wata rahama ba.”