✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gaggan ’yan siyasar Yamma sun hadu a Oyo don bikin tunawa da Lam Adesina

A ranar Litinin da ta gabata ce wasu fitattun ’yan siyasa daga jam’iyyu daban-daban a Kudu maso Yamma da suka ziyarci Ibadan domin halartar bikin…

A sahun gaba daga hagu Cif Bola Tinubu da Cif Bisi Akande da Gwamna Abiola Ajimobi na Oyo da takwaransa na Osun Rauf Aregbisola a taron tunawa da marigayi Lam Adesina.A ranar Litinin da ta gabata ce wasu fitattun ’yan siyasa daga jam’iyyu daban-daban a Kudu maso Yamma da suka ziyarci Ibadan domin halartar bikin tunawa da tsohon Gwamnan Jihar Oyo, Alhaji Lamidi Adesina wanda ya cika shekara daya da rasuwa. 

Wakilinmu ya ce, ba a ga Gwamna Abiola Ajimobi na Jihar Oyo a wurin bikin farko na kaddamar da gidauniyar tunawa da marigayin da aka gudanar a gidansa a Unguwar Felele ba. Sai dai an samu tabbaci daga ofishinsa cewa, rashin halartar tana da nasaba da rantsar da sababbin kwamishinoni da ya gudanar a daidai lokacin.
Babban dan marigayin, Dokta Ayobami Adesina ne ya jagoranci kaddamar da gidauniyar mai suna Ayo Lam Care Foundation, wacce ta samu halartar manyan mutane har da tsohon Gwamnan Jihar Adebayo Alao Akala.
Biki na biyu shi ne wanda aka gudanar a filin wasa na Lekan Salami da ke Adamasingba a Ibadan, inda manyan mutanen da suka halarci bikin suka hada da jagoran Jam’iyyar APC, kuma tsohon Gwamnan Legas, Bola Ahmed Tinubu da Shugaban Jam’iyar APC ta kasa Cif Bisi Akande da Gwamna Ra’uf Aregbesola na Osun da wakilan gwamnonin Legas da Ogun da Ekiti da tsofaffin gwamnonin Oyo Rashid Ladoja da Omololu Olunloyo da Cif Iyiola Oladokun wanda shi ne Mataimakin marigayi Gwamna Lam Adesina. Sarakuna ma ba a bar su a baya ba domin sun aika da wakilai zuwa wurin addu’o’I’n da aka yi wa marigayin.
Babban bako mai jawabi Sheikh Muhydeen Bello, ya tunatar da mahalarta ne musamman shugabanni da masu rike da mukamai da su nuna tsoron Allah wajen gudanar da jagorancin da suke yi wa jama’a. Shaihin malamin ya shafe awa daya yana wa’azi inda ya fi mayar da hankali a kan tunatarwa da yin koyi da irin jagoranci da mulkin adalci da marigayi Lam Adesina ya gudanar a lokacin yana raye.
Cikin jawabinsa Gwamna Abiola Ajimobi, ya ce ba zai taba mancewa da marigayi Lam Adesina ba, “Domin ni ne mutum na farko da na ci gagarumar moriya da marigayi Alhaji Lamidi Onaolapo Adesina ya bayar a kan harkokin siyasa a Jihar Oyo wacce ta kai ni ga rike mukamin Gwamna a yanzu.”
daruruwan mutane maza da mata ne suka samu halartar wannan biki da shi ne na farko da aka shirya domin tunawa da tsohon Gwamna Lam Adesina.