✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Galibin sarakunan gargajiya a Kuros Riba suna cikin kungiyoyin asiri – Shugaban Majalisa

Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kuros Riba, Mista Eteng Williams ya yi zargin cewa galibin sarakunan gargajiyar jihar suna cikin kungiyoyin asiri. “Idan basarake na cikin…

Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kuros Riba, Mista Eteng Williams ya yi zargin cewa galibin sarakunan gargajiyar jihar suna cikin kungiyoyin asiri. “Idan basarake na cikin kungiyar asiri ta yaya ake tsammanin zai sanar da hukuma su wane ne ’ya’yan kungiyar asirin idan suka yi ba daidai ba”? Ya yi tambaya. Shugaban Majalisar ya furta haka ne a jawabin da ya gabatar a taron da aka gudanar a Kalaba kan harkokin tsaro, matsalolinsa da kalubalen da ke cikinsa da wata tashar rediyo FM mai suna Sparking 92.3 da ke watsa shirye-shirye a Kalaba babban birinin Jihar Kuros Riba ta shirya.

Shugaban wanda dan Majalisar Jihar mai wakiltar Mazabar Boki ta Biyu, Mista Hilary Bisong ya wakilta, ya ci gaba da zargin sarakunan da cewa, “Mu yi wa kanmu adalci, matukar ana samun irin haka a masarautunmu me zai sa ba za mu rika samun kalubalen tsaro a cikinmu ba? Alhali ta yadda muka zabi shugabanninmu da sarakunanmu ba a zabe su ta tsari mai kyau ba da zai gina ingantaccen tsaro da zaman lafiya.”

Mista Williams ya kara da cewa, “Idan aka kwatanta kalubalen tsaro da muke da shi a yanzu da can baya za a ga yanzu al’amura sun riga sun tabarbare. “Yanzu a dukkan kananan hukumominmu shugabanninsu ba su yin taro a tattauna batun tsaro da kalubalensa. Matukar aka yi watsi da batun dole a ci gaba da fuskantar matsalolin tsaro,” inji shi.

Shugaban Majalisar ya ce gwamnati tana ware wa harkar tsaro a matakin kananan hukumomi kudi domin harkar tsaro a kananan hukumomin kuma suna yin taro kowace ranar Litinin domin tattauna halin da ake ciki idan har akwai kalubale ta nan ake tattauna yadda za a tunkare shi a yi maganinsa. Ya ce amma yanzu shiru ake ji taron na mako-mako an daina yinsa bare a tattauna wata matsala ta tsaro kamar yadda aka saba.

Sai dai Shugaban ya kare ’yan majalisar jihar inda ya ce “A matsayinmu na ’yan majalisa mun yi dokoki birjik da suka hada da dokar yaki da sace mutane ana karbar kudin fansa da kuma ta hana fataucin yara.”

Wadansu daga cikin mahalarta taro kan tsaron akwai jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi wato NDLEA da jami’an tsaro na sibil difens da sauransu.