✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gamayyar kungiyoyin Fararen Hula ta yi taro kan halin da kasa ke ciki

Wata sabuwar kungiya ta gamayyar kungiyoyin fararen hula ta yi taro a Kano, inda ta tattauna batun tattalin arziki da rashin tsaro da sauransu.A jawabin…

Wata sabuwar kungiya ta gamayyar kungiyoyin fararen hula ta yi taro a Kano, inda ta tattauna batun tattalin arziki da rashin tsaro da sauransu.
A jawabin maraba, Sakataren kungiyar Muryar Talaka, Malam Bishir Dauda Sabuwar Unguwa, ya nuna takaici kan tabarbare al’amarin tsaro da kuma gazawar gwamnati kan magance hare-hare da kisan dimbin ’yan Najeriya da ake yi a kullum.
Malam Bishir ya yi tir da lalacewar tattalin arziki, inda ya ce mutane suna cikin kunci da takura kuma suna rayuwa ta kaka-ni-ka-yi da tsananin talauci. Ya zargi Gwamnatin Tarayya da laifin jawo lalacewar harkar ilimi, indaya bayar da misali da yajin aikin malaman kwalejojin kere-kere na tarayya da ya jawo rufe kwalejojin na tsawon wata bakwai.
A jawabin da shugaban Rundunar Adalci ta Najeriya, Alhaji Abdulkarim dayyabu, ya yi suka ne kan yadda ’yan yankin Neja-Delta suke goranta wa ’yan Arewa cewa mai nasu ne. Ya ce doka ta nuna cewa duk wata dukiya ta karkashin kasa mallakar dukan ’yan kasa ne. Ya kuma kawo shawarar cewa kamata ya yi a debe ’yan Neja-Delta daga inda suke kukan mai ya gurbata, a mayar da su wani wurin kuma a gyara musu wurin don su ci gaba da rayuwa.
Alhaji Abdulkarim wanda ya gargadi shugabanni su ji tsoron Allah wajen ba talakawa hakkinsu, ya ce ya kamata su san cewa talakawa amana ce gare su. Ya ce halin da ake ciki na lalacewar abubuwa da zubar da jini sun faru ne a saboda yawan saba wa Allah da ake yi. Don haka ya yi kira ga jama’a su koma ga Allah.