✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ganawa da ’yar Najeriya da ta zo ta 10 a Musabaka ta Duniya ta Dubai

A watan da ya gabata ne aka gudanar da Musabakar Alkur’ani ta Duniya a birnin Dubai da ke kasar Hadaddiyar Daular Larabawa. A’ishat Muhammed Amin…

A watan da ya gabata ne aka gudanar da Musabakar Alkur’ani ta Duniya a birnin Dubai da ke kasar Hadaddiyar Daular Larabawa. A’ishat Muhammed Amin daga Jihar Oyo ce, ta wakilci Najeriya a  musabakar da daliban kasashen duniya suka fafata inda ta samo lambar yabo da fiye da Naira miliyan biyu. Bayan ta dawo  Najeriya Aminiya ta zantawa da ita kamar haka:

Aminiya: Yaya aka yi kika wakilci Najeriya a Musabaka ta Duniya?

To farko sunana A’ishat Muhammed Amin, a haife ni a Unguwar Sabo Ibadan a Jihar Oyo, kimanin shekara 18 da suka gabata. Ina karatu ne a makarantar Islamiyyah ta Dharu Dha’awah da ke nan Sabo mazaunin Hausawan Ibadan. Kafin in samu zuwa Musabakar Alkur’ani ta Duniya a kasar Dubai, sai da na fara wakiltar Jihar Oyo a Musabaka ta Najeriya inda na yi nasara na zo ta daya a haddar izifi 40 a Katsina. Na halarci musabakar izifi 60 da aka yi a Gombe inda na sake yin nasarar zuwa ta daya. Bayan tantancewar da masu shirya Musabakar suka yi mana ne, sai na fito a matsayin dalibar da za ta wakilci Najeriya a Musabakar Duniya da aka yi a Dubai, inda nazo ta 10. Aka ba ni kyautuka da satifiket da kimanin Naira miliyan biyu. Kafin mu kama hanyar zuwa Dubai sai da aka yi mini gyare-gyaren karatu. A can Dubai akwai wakilan kasashe da yawa da aka fara tantancewa kafin a fara Musabakar. An mayar da wasu kasashensu saboda ba su cancanta ba, inda wakilan kasashe 68 suka rage suka fafata a tsakaninsu. Kuma an yi amfani da Alkur’ani irin na Madina ne wajen jarrabawa hawa-hawa, Allah Ya ba ni sa’a nazo ta 10.

Wane farin ciki kika ji kan nasarar da kika samu?

Alhamdulillahi, ina godiya ga Allah (SWT) da Ya ba ni sa’ar wakiltar kasar haihuwata Najeriya zuwa wajen  Musabakar ta Duniya. Wani abin mamaki shi ne irin yadda ’yan Najeriya da na kasar Dubai suka rika bugo min waya suna taya ni murna ba tare da mun san juna ba.  Wannan abin farin ciki ne kwarai musamman daukakar da Najeriya ta samu a idon duniya a dalilin wannan Musabaka. Kuma ina mika godiya ta ga iyayena musamman mahaifina Ustaz Muhammed Amin, wanda ya yi min rakiya zuwa Dubai da malaman makarantarmu ta Darud Da’awa da ke Sabo Ibadan da dukkan daliban makarantar da ’yan uwa Musulmin Jihar Oyo da kasa baki daya.

Wane kira kike da shi ga dalibai ‘yan uwanki?

A’ishat: Muhimmin abin da nake son tunatar da dukkan dalibai Musulmi a Najeriya shi ne mun fi mayar da hankali a kan ilmin boko fiye da ilimin addinin Musulunci musamman karatun Alkur’ani. Wannan babbar illa ce, ga rayuwarmu a nan duniya da gobe Kiyama. A lokuta da yawa idan dalibai suna da jarrabawar boko sai ka ji sun ce sun daina karatun hadda wanda yin haka ba daidai ba ne domin idan akwai karatun Alkur’ani a tare da kai to zai taimaka wa kwakwalwarka wajen fahimtar komai na rayuwar duniya cikin sauki. Kuma shi ne zai daukaka darajarka a cikin iyaye da kakanni da soyayyar jama’a gare ka. Saboda haka nake kira ga ’yan uwa Musulmi mu rungumi karatun Alkur’ani hannu bibbiyu mu daina wasa da shi.