✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ganduje ya bude wani sabon bincike kan Sarkin Kano

Gwamnatin jihar Kano ta bude wani sabon bincike kan Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, inda hukumar yaki da rashawa ta jihar ke binciken masarautar Kano…

Gwamnatin jihar Kano ta bude wani sabon bincike kan Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, inda hukumar yaki da rashawa ta jihar ke binciken masarautar Kano kan zargin an sayar da wani fili mallakar masarautar, a cewar bayanan da Aminiya ta tattaro. 

Wasu takardun bayanai da jaridar ta gani sun bayyana cewa masarautar ta kulla yarjejeniya da wani kamfani mai suna Capital Properties Nigeria Limited (CPNL), domin gina filin da ke unguwar Hotoro a Karamar Hukumar Nasarawa wanda kuma ake yi wa lakabi da Gandun Sarki.

An kulla yarjejeniyar ne ta hanyar wani kwamitin mutum shida da masarautar ta kafa karkashin jagorancin Jarman Kano, Farfesa Isa Hashim.

Sai dai hukumar ta shaida wa Aminiya cewa, ta kama mambobin kwamitin guda biyu, “Bisa zargin karbar cin hancin Naira miliyan 20 a matsayin wakilan Sarki sannan kuma za ta kai su kotu kan zargin kwace da kuma karbar na-goro.”

Da aka tuntube shi kan batun, Farfesa Isa Hashim ya ce, ba zai iya cewa komai ba, masarauta ce kadai za ta iya magana. Sai dai har yanzu masarautar ba ta ce komai ba game da batun.

Wannan sabon binciken yana zuwa ne kwanaki kadan da tabbatar da zaben Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, da Kotun Kolin Najeriya ta yi, kuma wasu na ganin wannan binciken ci gaba ne kan takun sakar da ke tsakanin Sarki da gwamnan jihar, wanda ya kai ga gwamnan kirkirar sabbin masarautu hudu a jihar.

Gandun Sarki

Bisa al’ada, Gandun Sarki wata gona ce da mai martaba sarki ya kebance domin aiyukan noma a fadin jihar. Bayan na Hotoro, an yi zargin cewa masarautar ta sayar da wani filin a unguwar Bubbugaje da ke Karamar Hukumar Kumbotso.

An ce, an sayar da filin na Bubbugaje ne ga kamfanin CPNL kan kudi Naira miliyan 70. Kazalika aka ce an tsaga filin zuwa kananan filaye kan Naira miliyan 1.1 da kuma Naira dubu 360, kan kowane fili – ya danganta da girmansa.

Har wa yau, majiyarmu ta gano cewa an saka kudin filin na Bubbugaje ne a asusun masarauta bayan kammala ciniki tsakanin kwamitin Isa Hashim da kamfanin CPNL.

A gefe guda kuma, an yi zargin cewa an sayar da Gandun Sarki na Hotoro kan Naira miliyan 80 amma miliyan 55 kawai aka biya masarautar.