✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ganduje ya gindaya sharudda akan sulhunsu da Sarkin Kano

Gwamnan Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya gindaya wasu sharudda  ga Sarki Sanusi wanda ya ce su ne, matakin tabbatar sulhu tsakaninsa da Sarkin na…

Gwamnan Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya gindaya wasu sharudda  ga Sarki Sanusi wanda ya ce su ne, matakin tabbatar sulhu tsakaninsa da Sarkin na Kano.

Gwamna Ganduje ya bayyana hakan ne a wata takarda mai dauke da sa hannun Kwamishinan Watsa Labarai na Jihar Kano Kwamared Muhammad Garba. Daga cikin sharuddan da Gwamna Gandujen ya gindaya wa Sarkin, akwai batun cewa sai Sarkin Kanon ya fito fili ya nemi afuwar Gwamnan tare da al’ummar Jihar Kano game da wulakanta darajar Masarautar Kano da ya yi ta hanyar tsoma baki a harkar siyasa.

Har ila yau Gwamnan Ganduje ya bayyana cewa, akwai bukatar Sarkin ya yi mu’amala ta aiki da sabbin Sarakunan masarautun da aka kirkira guda hudu a matsayinsa na Shugaban Sarakunan.  “Akwai bukatar Sarkin ya yi amfani da gogewarsa wajen jagorantar sabbin Sarakunan tare da ganin sun yi abin da ya kamata wajen ciyar da Jihar gaba ta fuskar zamantakewa da tattalin arziki”.