✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ganduje ya kaddamar da shirin tallafawa tsangayoyi da Islamiyoyi

Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Ganduje ya kaddamar da shirin tallafawa tsangayoyi da  makarantun Kur’ani da Islamiyoyin jihar. Gwamnan, ya kaddamar da shirin a jiya…

Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Ganduje ya kaddamar da shirin tallafawa tsangayoyi da  makarantun Kur’ani da Islamiyoyin jihar.

Gwamnan, ya kaddamar da shirin a jiya Lahadi wanda ya bayyana a matsayin kokarin da suke na bada ilimi kyauta a matakan makarantun firamare da sakandire wanda hakan zai rage yawan yara masu gararamba a cikin garin.

“Mun yi wa Allah godiya da ya bamu ikon kaddamar da wannan shirin na tallafawa makarantun Islamiyoyi ta hanyar raba kayan abinci da kuma kudi ga alarammomi 1,000 daga tsangayoyi 1000 a  duk fadin kananan hukumomi 44 na jihar.”

Gwamna Ganduje, ya jinjina wa kokarin da gidauniyyar Hukumar raya kasashen ta Biritaniya DFID, Babban Bankin Duniya da kuma sasshen tallafawa yara na majalisar dinkin duniya wato UNICEF.