✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ganduje ya nada Aminu Ado Bayero Sarkin Bichi da wasu Sarakuna 3

Gwamnatin jihar Kano ta nada Alhaji Aminu Ado Bayero, dan marigayi tsohon sarkin Kano Ado Bayero a matsayin sabon sarkin Bichi. Sannan daga bisani an…

Gwamnatin jihar Kano ta nada Alhaji Aminu Ado Bayero, dan marigayi tsohon sarkin Kano Ado Bayero a matsayin sabon sarkin Bichi. Sannan daga bisani an tabbatar da Hakiman masarautun Karaye da Rano da Gaya a matsagyin sabbin sarakuna masu daraja ta daya.

Kwamishinan watsa labarai na jihar Kano Malam Muhammad Garba, ne ya sanar da hakan yau Juma’a kuma ya ce, sabbin sarakunan zasu karbi takardar shaidar zama sarakuna masu daraja ta daya a gobe Asabar a filin wasa na Sani Abacha da ke Kano.

Sabbin Sarakunan masu daraja ta daya.

  1. Sarkin Gaya – Alhaji Ibrahim Abdulkadir Gaya
  2. Sarkin Rano – Alhaji Tafida Abubakar Ila
  3. Sarkin Karaye – Dr. Alhaji Ibrahim ll
  4. Sarkin Bichi – Alhaji Aminu Ado Bayero