Da Dumi Dumi

Ganduje ya nada sabon Sarkin Rano

Sabon Sarkin Rano, Alhaji Kabiru Muhammadu Inuwa

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya nada Alhaji Kabiru Muhammadu  Inuwa, Hakimin  Kibiya, a matsayin sabon Sarkin Rano.

Alhaji Kabiru Muhammadu Inuwa ya cike gurbin da marigayi tsohon sarkin Rano Alhaji Tafida Abubakar ya bari bayan Allah Ya yi masa rasuwa a makon jiya.

tsohon sarkin Rano ya rasu ne cikin ‘yan awwani bayan an kwatar da shi a Asibiti,kuma zuwa wannan lokacin babu bayanin musababbin mutuwar sa.

Marigayin shine sarkin Rano na farko, bayan da gwamna Ganduje ya samar da karinmasarautu hudu masu daraja ta daya a jihar Kano.

 

ADVERTISEMENT
Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya