✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ganduje ya nada Sarki Sanusi Shugaban Majalisar Sarakunan Kano

Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya nada Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, a matsayin shugaban Majalisar Sarakunan Gargajiya ta jihar.  Nadin Sarkin zai…

Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya nada Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, a matsayin shugaban Majalisar Sarakunan Gargajiya ta jihar.  Nadin Sarkin zai fara aiki ne daga yau Litinin 9 ga watan Disamba 2019.

A wata sanarwa da babban sakataren hulda da ‘yan jaridu na gwamnan, Abba Anwar, ya fitar a tsakar daren da ya gabata, ya ce, bisa tanadin sashe na 4 (2) (g) da sashe 5 (1) (2) na dokar masarautun jihar ta 2019, Gwamnan jihar ya nada, Alhaji Muhammadu Sanusi na II, Sarkin Kano a matsayin Shugaban Majalisar Sarakunan.

Sanarwar ta kara da bayyana cewa, daga cikin sauran ‘yan majalisar akwai dukkanin sauran sarakunan jihar masu daraja ta daya, na Bichi da Rano da Karaye da Gaya, Alhaji Aminu Ado Bayero, Alhaji Dr Tafida Abubakar (Autan Bawo), Alhaji Dr Ibrahim Abubakar II da kuma Alhaji Ibrahim Abdulkadir.