✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ganduje zai yi nadama a karshen gwamnatinsa – Kwankwaso

Tsohon gwamnan Kano Rabi’u Musa Kwankwaso ya bayyana cewa mutumin da ya gaje shi Gwamna Abdullahi Umar Ganduje tare da mukarabbansa za su yi nadama…

Tsohon gwamnan Kano Rabi’u Musa Kwankwaso ya bayyana cewa mutumin da ya gaje shi Gwamna Abdullahi Umar Ganduje tare da mukarabbansa za su yi nadama da zarar gwamnatinsu ta kare.

Injiniya Kwankwaso ya ce gwamnatin jihar mai ci a yanzu tana gudanar da al’amuran mulkinta ne cikin karairayi da yaudara wanda hakan ne zai sanya gwamnan nadama da zarar ya kammala mulki.

“Za su yi nadama da danasanin cewa da sun baiwa wanda ya lashe zaben 2019 mulki,” kamar yadda ya fada a hirarsa da wasu gidajen rediyo a Kano.

Sanata Kwankwaso ya ce ai duk wadanda ma suke barin tafiyarsa ta siyasa burinsu shi ne “su zama kamar Rabi’u Kwankwaso”.

A lokacin da Ganduje ke karbar shugaban jam’iyar PDP na jihar wanda ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC Rabiu Sulaiman Bichi ya bayyana cewa burin Kwankwaso shi ne ya tsaya takarar shugaban kasa, inda ya bayyana shi a matsayin dan siyasa da ba shi da kwarewa, wanda bai san komai ba”.

“Na san Kwankwaso fiye da kowa, mutum ne mai nuna ya fi kowa sani da iyawa, duk abin da zaka yi masa ba zaka burge shi ba, mutum ne mai son kai, nayi hakurin jure munanan hallayarsa a lokacin da muke tare” in ji Ganduje.

Ya zargi Rabi’u Kwankwaso da cewa “ya kankane komai babu wanda yake taimakawa, hatta yawon kamfe da muka yi bai bayar da ko kwandalarsa ba”.

A martaninsa, shi kuma tsohon gwamnan cewa ya yi: “Ni burina a rayuwa duk wanda yake tare da ni tun daga kan dan aike shi ne in daga shi ya zama babba [Chief Exectuive Officer] a Turance.”

A karshe Kwankwaso ya nanata cewa ba shi ne ya haddasa rikicin da yake tsakaninsa da Ganduje ba sannan ya ce yana ci gaba da yin hakuri a matsayinsa na shugaba.

Ana cigaba da samun musayar yawu tsakanin gwamnan Kano mai ci da tsohon gwamna Kwankwaso tun bayan da kotun koli ta tabbatar wa Gwamna Ganduje kujerarsa.