✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gangamin PDP na Minna: Mu’azu da Jonathan sun saba wa juna

Shugaban Jam’iyyar PDP na kasa Alhaji Ahmadu Adamu Mu’azu da Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan sun yi jawabai masu karo da juna a wurin gangamin…

Shugaban Jam’iyyar PDP na kasa Alhaji Ahmadu Adamu Mu’azu da Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan sun yi jawabai masu karo da juna a wurin gangamin PDP na shiyyar Arewa ta Tsakiya da aka gudanar a Minna fadar Jihar Neja, game da gwamnonin da suka bar jam’iyyar zuwa Jam’iyyar APC.
A jawabin Alhaji Ahmadu Mu’azu, a wurin gangami da aka gudanar a filin Kasuwar Duniya da ke Anuduwar Shango, ya bukaci Gwamnan Jihar Neja Dokta Mu’azu Babangida Aliyu wanda ya zama jagoran gwamnonin a wancan lokacin cewa ya yi amfani da damar da yake da ita ya shawo kansu su dawo Jam’iyyar PDP.
Alhaji Ahmadu Mu’azu, ya tabbatar wa gwamnonin cewar kofar jam’iyyar a bude take domin su dawo cikinta tare da bayar da gudunmawarsu bisa la’akari da cewa su mutane ne masu hangen nesa domin a hada karfi da karfe ta yadda za a dora daga ci gaban da aka samu a mulkin jam’iyyar na shekara 15.
Sai dai da Shugaba Goodluck Jonathan yake gabatar da jawabinsa, ya shaida wa taron cewa a halin da ake ciki jam’iyyar ba ta bukatar gwamnonin da suka koma jam’iyyar adawa ta APC, domin a cewarsa ba su bukatar jam’iyyar da suka taimaka aka gina ta kuma ta samu karbuwa a tsakanin ’yan Najeriya shekara 14 da suka gabata, inda suka gwammace su sake gina wata jam’iyyar da ba ta da alkibla.
Shugaba Jonathan ya kwatanta gwamnoni da masu dabi’ar hawainiya da ba a san ainihin launinsu a fannin siyasa ba, inda ya ce farin jinin Jam’iyyar APC bai wuce a kafofin watsa labarai ba.
Tsohon shugaban jam’iyyar Ahmadu Ali, ya bayyana wa taron cewa ayyukan da gwamnatin Shugaba Jonathan ta gudanar a sassan kasar nan, sun isa zama hujjojin da za su sa ya sake tsayawa takarar shugabancin kasar nan a shekara mai zuwa.