✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ganin karshe da aka yi wa Abba Kyari

Gani na karshe da aka yi wa Mallam Abba Kyari a bainar jama’a shi ne ranar 20 ga watan Maris, lokacin da aka ce an…

Gani na karshe da aka yi wa Mallam Abba Kyari a bainar jama’a shi ne ranar 20 ga watan Maris, lokacin da aka ce an gan shi tare da shugaban kasa a masallacin Juma’a.

Kafin nan, a ranar 14 ga watan Maris shugaban ma’aikatan na Fadar Shugaban Kasa ya dawo daga wata tafiya da ya yi Jamus, inda ya wakilce gwamnatin Najeriya wajen sanya hannu a kan wasu yarjejejniyoyi.

Kafin a ba da sanarwa cewa ya kamu da cutar coronavirus kwana 10 bayan nan kuma, ranar 24 ga watan Maris, ya halarci wasu wurare ya kuma gudanar da wasu ayyuka na gwamnati da ma na kashin kansa.

Jim kadan bayan dawowarsa daga Jamus, marigayi Malam Abba Kyari ya halrci daurin auren dan Sufeto Janar na ’Yan Sanda Muhammad Adamu tare da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano da hamshakin attajiri Aliko Dangote da sauran manyan mutane.

Sannan a ranar 16 ga watan Maris ya halarci wata ganawa tsakanin Shugaba Muhammadu Buhari da gwamnonin jam’iyyar APC, har ma ya dauki hoto da gwamnaonin bayan an gama.

Gwamnonin da suka halarci taron su ne Babagana Zulum na jihar Borno, da Babajide Sanwo-Olu na Jihar Legas, da Dapo Abiodun na Jihar Ogun, da Godwin Obaseki na Jihar Edo, da Atiku Bagudu na Jihar Kebbi, da Muhammad Badaru Abubakar na Jihar Jigawa.

Sauran su ne Abdulrahman Abdulrazaq na Jihar Kwara, da Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa, da Abubakar Sani Bello na Jihar Neja, da Simon Lalong na Jihar Filato.

Sai kuma Rotimi Akeredolu na Jihar Ondo, da Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano, da Adegboyega Oyetola na Jihar Osun, da Aminu Bello Masari na jihar Katsina, da Hope Uzodinma na Jihar Imo, da kuma Inuwa Yahaya na Jihar Gombe.

Kafin wannan taro, a ranar ta 16 ga watan Maris, marigayin ya gana da shugaban jam’iyyar APC Adams Oshiomhole.

Ranar 17 ga watan Maris kuma ya jagoranci wata tawagar gwamnatin tarayya da ta ziyarci jihar Kogi don yin ta’aziyya ga iyalan Gwamna Yahaya Bello wanda mahaifiyarsa, Hajiya Hauwa’u Ozoho, ta rasu.

A ranar 18 ga watan na Maris ne kuma marigayin ya halarci zaman Majalisar Zartarwa ta Tarayya.

Sannan a ranar 19 ga wata ya halarci wani taro na kaddamar da wani kwamitin gudanarwa a kan ayyukan jinkai.

A ranar 24 ga wata aka sanar da cewa marigayin na dauke da cutar coronavirus wadda ake kyautata zaton ya kamu da ita yayin ziyar da ya kai Jamus da Masar.