✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Garabasar da ke tare da sayen Hannun Jari

Na samu wasiku da yawa a kan tambayoyi da neman shawarwari game da sayen hannun jari, tun daga karshen shekarar da ta gabata ya zuwa…

Stock Exchange

Na samu wasiku da yawa a kan tambayoyi da neman shawarwari game da sayen hannun jari, tun daga karshen shekarar da ta gabata ya zuwa yau. To na lura cewa wannan lokaci ne da kasuwar hannun jari ta fara farfadowa, tun shekara kimanin uku wadanda hannayen jarin suka yi ta faduwa masu su kuma suka rika yin asara inda wadansu hannayen jarin suka yi faduwar da darajarsu ba ta kai ta takardar da aka rubuta su a kai ba.
Ban yi saurin amsa wadannan tambayoyi ba, ko in ba masu neman shawara irin shawarwarin da su ke bukata ba, saboda duk mai bin wannan shafin a wannan shekarun zai san na yi kasidu da yawa a kan al’amura da yawa da suka jibanci harkar hannun jari. Na kuma yi makala a karshen shekarar da ta gabata a kan yadda ’yan kasuwa za su dawo kasuwar hannun jari a lokacin da ta fara farfadowa, da kuma wadanne irin hannayen jari dan kasuwa zai saya a wannan lokaci domin samun amfanin wannan garbasa.
Wadansu tambayoyin da neman shawarwari sun zo min a cikin watani biyu na baya, a lokacin da na ke jeranta makalar shawarwari ga dan kasuwa a kan shugabanci. Ban iya na katse wannan makala ba domin fuskantar wadannan bukatu. Wadannan tambayoyi da neman shawarwari sun jibanci alfanu, ko rashinsa, game da sayen hannun jari a kowanne lokaci. To, ba zan fasa jan kunnen mai niyyar sayen jari, kamar yadda na saba yi ba,  kafin in fara cewa kada kudin da za a sayi hannun jari su kasance kudin da dan kasuwa ke amfani da su ne yau da kullum. Misali, jarinsa da yake juyawa a harkar da yake yi, ko kudin da yake yin hidimominsa na yau da kullum, kamar kudin abincin iyalinsa da kudin makarantar ’ya’yansa, ko kudin da zai biya hayar gidansa ko na shagon da yake gudanar da harkarsa. Kudin da dan kasuwa zai sayi hannun jari, kudi ne da dan kasuwa zai ajiye domin wata bukata a gaba.
Jarin da aka sayi hannun jari, jari ne da dan kasuwa zai iya lura da habakarsa a kowanne mako, inda zai iya kiwonsu tamkar awaki. Wato zai kiyaye jarinsa yayin da zai iya lura da farashin kamfani ko kamfanonin da dan kasuwa ya zuba jarinsa; zai iya janyewa daga kamfanin da ya ga babu alheri cikinsa ya mayar inda yake ganin ya fi alfanu. Wannan garabasa ce da ba a samunta a sauran kafofi na kasuwanci kamar harkar kasa, wato saye da sayar da fulotai da gidaje da kuma sauran harkoki.
Hannun jari na iya ba dan kasuwa damar samun riba daga kamfanonin da kwararru ke tafiyar da su ake samun ingantacciyar riba. Idan ba ta hanyar sayen hannun jari ba, dan kasuwa mai karamin jari ba zai iya tsara kamfani  har ya dauki ma’aikata kwararru  masu basira har ya amfana ba. Da kudi kalilan dan kasuwa zai iya sayen jarin kamfanonin man fetur ko na masana’antu ko na bankuna, da sauransu.
Zuba jari a kamfanoni ta kafar hannun jari harka ce da ke samun kulawar kwararru daga farkon ta, yayin da dan kasuwa ya tuntubi wakilinsa na sayen hannun jari wanda zai yi masa bayani a kan hannun jarin da zai saya. Kuma akwai bayanai a kasidu da mujallu akai-akai a kowanne lokaci a kan kamfanonin da suke da jarikansu a kasuwa, har ma da bayanai a kan irin rukunin wadannan kamfanonin. Wannan zai sa dan kasuwa sukunin samun shawarwarin kwararru a farashi kalilan. Wannan zai ba dan kasuwa samun riba mai tsoka, ya kuma kare su daga munmunar asara.
 Zan tashi daga nan idan Allah Ya kai mu mako mai zuwa.