Gare ki uwar ’ya’ya (Biyayya ga iyaye da sadar da zumunta)

Assalamu alaikum warahmatullah.

Wannan ne karo na hudu na wannan tunatarwa da muke yi miki ya ke uwar ’ya’ya! Burinmu da hakan ki samar da al’umma tagari wadda za a yi alfahari da ita a duniya da Lahira. A yau za mu tabo wasu muhimman abubuwa da suke taimakawa a samu al’umma mai tsari abar sha’awa. Wato koyar da biyayya ga iyaye da sadar da zumunta a tsakanin yara.

 

Biyayya ga iyaye:

Biyayya ga iyaye tana daga cikin manyan farillai da wajibai a kan dan Adam. Ita ce mafi girman ayyukan da’a baya ga bauta ga Allah ba tare da yi maSa shirka ba, kamar yadda Allah Ya ce: “Ku bauta wa Allah kada ku yi maSa shirki da komai. Kuma ga iyaye ku kyautata.” (Nisa’i: 37).

ADVERTISEMENT

Kuma da aka tambayi Annabi (SAW) mafiya soyuwar ayyuka a wurin Allah sai ya ce: “Yin Sallah a kan lokacinta. Aka ce sai me? Ya ce: “Yin biyayya ga iyaye.” Aka ce sai wane? Ya ce: “Jihadi a tafarkin Allah” (Muttafakun alaihi).

Don haka a matsayinki ta uwa ki tabbatar kin koya wa ’ya’yanki cewa biyayya ga iyaye ibada ce da Allah Ya yi umarni da ita, kada su dauka wayo ake yi musu don a tankwara su. Ki rika nuna musu umarni ne na Allah ta hanyar kawo musu hujjoji daga Littafin Allah da Hadisan Manzon Allah (SAW) da misalan mutanen kwarai. Ki nuna musu wasiyyar da Allah Ya yi ga ’ya’ya game da mahaifansu kamar fadinSa Madaukaki: “Kuma Mun yi wasiyya ga mutum game da iyayensa, mahaifiyarsa ta dauke shi wahala kan wahala ta kuma shayar da shi na shekara biyu, (don haka). Ka gode Mini kuma ka gode wa iyayenka, gare Ni makoma take.” (Lukman: 14). Da kuma inda Ya yi umarnin a kyautata musu musamman idan suka tsufa. “Ubangijinka Ya hukunta cewa kada ku bauta wa kowa face Shi. Kuma game da iyaye ku kyautata, koda dayansu ya tsufa ko dukkansu biyu, kada ka ce musu tir! Kuma kada ka yi musu tsawa, ka gaya musu magana mai dadi. Ka tausasa musu fika-fikan iyakar rahama kuma ka ce: “Ubangiji Ka yi musu rahama Ka tausaya musu kamar yadda suka raine ni ina karami.” (Isra’i: 23-24).

Ki nuna musu cewa Annabi (SAW) ya yi Allah wadai da wanda bai yi wa iyayensa abin kirkin da zai kai shi ga Aljanna ba. Ya ce: “Allah Ya turbuda hancinsa, sannan Allah Ya turbuda hancinsa, sannan Allah Ya turbuda hancinsa!” Sai aka ce wane ne ya Manzon Allah?” Ya ce: “Wanda ya riski mahaifansa lokacin tsufarsu ko daya daga cikinsu ko dukkansu biyu, amma bai shiga Aljanna ba.” Muslim.

Ki nuna musu Annabi (SAW) ya nuna rashin biyayya ga iyaye yana daga cikin manyan zunubai, inda a wani Hadisinsa (SAW) ya nuna a manyan zunubai daga shirka sai saba wa iyaye. Wannan yana nuna bayan hakkin Allah sai hakkin mahaifa. Kuma wajen hakkin uwa ce a gaba kamar yadda wani Hadisi ya nuna Annabi (SAW) ya ambaci uwa sau uku kafin uba.

Kyautata wa iyaye dole ne koda kafirai ne, kuma wajibi ne a yi musu biyayya a cikin komai in ba sabon Allah ba ne. Wajibi ne a dadada musu a kyautata musu a kyautata wa wanda suke so a kyautata masa, a yi komai da zai sa su ji dadi su samu natsuwa da farin ciki matukar abin nan ba sabon Allah ba ne.

Sadar da zumunta:

Baya ga biyayya da kyautata wa iyaye, akwai kuma hakkin sadar da zumunta wato a rika kyautata wa dangin uwa da na uba. Kada a matsayinki ta uwa ki yarda ki nuna wa ’ya’yanki ’yan uwanki kawai. Ki tabbata suna ziyarta da kyautata wa dangin mahaifinsu da naki dangin. Ki nuna musu ayoyi da hadisan da suka yi magana kan sadar da zumunta da illar yanke zumunta wadda take haifar da barna babba a tsakanin al’umma.

Allah Madaukaki Ya ce: “Wadanda suke sadar da abin da Allah Ya ce a sadar (na zumunta).…” (Suratur Ra’ad: 21).

Kuma Ya ce: “Ku bauta wa Allah, kada ku hada Shi da kowa. Iyaye kuma ku kyautata musu da ’yan uwanku na kusa….” (Suratun Nisa’i: 36). Annabi (SAW) ya ce: “Wanda ya kasance ya yi imani da Allah da Ranar Lahira, to ya sadar da zumuntarsa.” (Muttafakun alaihi).

Kuma Annabi (SAW) ya ce: “Zumunta tana makale da Al-arshin Ubangiji, tana cewa: (Ya allah) wanda ya sadar da ni, Ka sadar da shi (da rahamarka). Wanda ya yanke ni Ka yanke shi (daga rahamarka).” Buhari da Muslim

Ya ke uwa! Ki tuna akwai alheri mai yawa a cikin sadar da zumunta kamar karuwar albarka a cikin rayuwa da samun natsuwa da kula da halayen dangi da yin sadaka ga fakiran cikinsu da yin ludufi ga masu dukiyarsu da girmama tsofaffinsu da tausaya wa kananansu da shirya musu liyafar girmamawa da yin haba-haba da su da tarayya da su a cikin abubuwan farin cikinsu da taya su bakin ciki a abin da ya shafi bakin ciki da yi musu addu’a da amsa kiransu da yin tarayya da su a komai na dadi ko marar dadi.

Sadar da zumunta na haifar da kiyayewar Allah ga bawa, ya sa mutum ya samu alheri da ludufin Allah. Annabi (SAW) ya ce: “Zumunta tana makale da Al-arshi, tana cewa: “Wanda ya sadar da ni, Allah Ka sadar da shi (da rahamarka). Wanda ya yanke ni Allah Ka yanke shi (daga rahamarka).” Muslim. Kuma Annabi (SAW) ya ce: “Duk wanda yake son Allah Ya shimfida (Ya yalwata/Ya yawaita) masa arzikinsa kuma Ya albarkaci bayansa (’ya’yansa). To ya sadar da zumuntarsa.” (Muttafakun alaihi). Ya ke uwar ’ya’ya! Idan kina son ’ya’yanki su zamo masu arziki, masu nisan kwana masu aminci masu samun nasara a rayuwa, to ki tabbatar suna sadar da zumuntarsu, kada ki kuskura ki raba kan ’ya’yanki da na kishiyarki. Kada ki kuskura ki raba ’ya’yanki da dangin mijinki saboda yana da hannu da shuni ko wata daukaka ta duniya.

Domin yanke zumunta na jawo la’ana daga Allah, idan kuma Allah Ya la’anci mutum, to, karshensa ba zai yi kyau ba. Allah Madaukaki Yana cewa:  “Shin ba ku jin tsoron idan kuka saba kuka juya baya (ga dokokin Allah), ku yi ta barna a cikin kasa kuma ku yanke zumuntarku. Wadannan (masu barna da yanke zumunta) su ne wadanda Allah Ya la’ance su, kuma Ya kurmantar da su, kuma Ya makantar da idanuwansu.” (Suratu Muhammad: 22- 23). Kuma Annabi (SAW) ya ce: “Mai yanke zumunta ba zai shiga Aljanna ba.” (Muttafakun alaihi). Akwai gargadi mai tsoratarwa a wannan aya ya ke uwar ’ya’ya! Game da munin yanke zumunta don haka ki dora ’ya’yanki a hanyar raya zumunta a tsakaninsu da ’yan uwansu na haihuwa wato ’ya’yan kishiyoyinki da sauran dangin miji domin su tsira a duniya da Lahira.

Share