Search
Subscribe
Gare ki uwar ’ya’ya (Tausayi da Cika alkawari)

Gare ki uwar ’ya’ya (Tausayi da Cika alkawari)

Assalamu alaikum warahmatullah. A ci gaba da darasinmu mai take na sama yau za mu duba wasu kyawawan siffofi ne da ake so uwar ’ya’ya ta siffantu da su kuma ta dora ’ya’yanta a kansu. Wadannan siffofi su ne TAUSAYI (RAHAMA) da CIKA ALKAWARI:

 

Wajibi ne uwar ’ya’ya ta nuna wa ’ya’yanta tausayawa a cikin duk abin da take yi musu ko take sanya su aikatawa. Kada ta dora wa yara nauyin da ba za su iya dauka ba. Kada ta sanya su yin aikin da ya fi karfinsu, kada ta mayar da su bayi masu nemo mata kudi ta hanyar dora musu talla da safe da rana da yamma, ta yadda ba damuwarta su samu ilimin addini da na zamani ba. Kuma kada ta yarda mahaifinsu ya mayar da su tamkar hanyar ci gaba da gina kansa koda ’ya’yansa za su rasa tasu makomar.

Sannan uwa ki tabbatar kin dora ’ya’yanki a kan dabi’ar rahama da tausayi da saukaka wa na kasa da su. Su kasance masu tausayin juna masu saukawa wa juna a cikin komai. Idan aka samu wannan rahama a tsakanin yara sai ta yadu tun daga gida zuwa unguwa zuwa gari zuwa kasa zuwa duniya baki daya.

Rahama ita ce babbar ginshikin aiko Annabi (SAW) da saukar masa da Alkur’ani. Allah Madaukaki Ya ce: “Ba Mu aiko ka ba, face rahama ga dukkan halitta.” (Anbiya’i: 107) Kuma Ya sake cewa: “Saboda wata rahama daga Allah ka saukaka (sanyaya) musu. Da ka kasance mai kaushi da zafin zuciya da sun gudu daga gare ka.” (Al-Imrana:159).

Rahama siffa ce daga cikin siffofin Allah kamar yadda Allah Madaukaki Ya ce: “RahamaTa ta yalwaci komai.” (A’arafi: 157). Kuma daga cikin sunayenSa Madaukaki akwai: “Mai rahama” da “Mai jinkai.”

Annabi (SAW) ya kwadaitar kan yin rahama da saukaka wa mutane inda ya ce: “Wanda ba ya rahama wa mutane, Allah ba zai yi masa rahama ba.” (Muttafakun). Kuma (SAW) ya ce: “Ku rahama (ku ji tausayi) ga wadanda suke cikin kasa, sai Wanda Yake cikin sama Ya yi muku rahama.” (Abu Dauda da Tirmizi).

Musulunci addini ne na rahama da tausayi da jinkai da sassauci hatta a fagen yaki, balle a rayuwar yau da kullum. Anas dan Malik (RA) ya ce duk lokacin da Annabi (SAW) zai tura Musulmi wurin yaki yakan ce: “Ku tafi da sunan Allah, kuma bisa dogaro ga Allah a kan akidar Manzon Allah. Kada ku kashe tsoho tukuf kada ku kashe yaro karami kada ku kashe mace kada ku yi guluwi ku tattara ganimarku ku gyara kuma kyautata, lallai ne Allah Yana son masu kyautatawa.” Abu Dawud

Akwai lokacin da Annabi (SAW) ya iske gawar wata mace a wani yaki, sai ya tsaya a kanta ya ce: “Bai kamata a kashe wannan ba.” Kuma ya taba tura wani sahabinsa cewa “Ka riski Khalid bn Walid cewa kada ya kashe zuriya ko dan kwadago ko mace.” Ahmad da Abu Dawud.

Shin ya ke uwa! Da iyaye sun koyar da ’ya’yansu wannan dabi’a ta tausayi da rahama da saukakawa zai yiwu wani ya dasa bam a kasuwa ko masallaci ko coci ko asibiti ko tashar mota da sunan yi wa addini aiki? Duk wanda ya dasa bam so yake kowa ya mutu, alhali wanda ya zo da addinin (SAW) ya hana kashe jinsin wadansu mutane koda a fagen daga ne, to ina ga wanda zai kashe mutanen da suka je kasuwa sayayya ko suka je tashar mota ko suka je asibiti? Wannan kaushin zuciya da rashin tausayi da rashin rahama ne suka yi wa mai yin haka tsatsa a zuciya.

Ba dan Adam ba hatta dabbobi Musulunci ya bukaci a tausaya musu misali Hadisi ya nuna an sanya wata mata a wuta saboda ta daure kyanwa ta hana ta abinci har ta mutu. Kuma ko a lokacin da za a yanka dabbobi an wajabta tausaya musu. Manzon Allah (SAW) yana cewa: “Lallai Allah Ya hukunta kyautatawa a cikin komai. Idan za ku yi kisa, to ku kyautata kisan. Idan za ku yanka dabba ku kyautata yankar, dayanku ya wasa wukarsa don ya hutar da abin yankarsa.” (Muslim).

Kisa shi ne abu na karshe da wani dan Adam zai aikata ga dan uwansa, amma duk da haka shari’ar Musulunci ta ce a kyautata kada a munana don a wahalar, wannan shi ne kaiwa karshe wajen tausayawa.

 

Cika alkawari:

Musulunci yana son a gina al’umma mai cika alkawari da mutunta yarjejeniya. Wajibi ne a matsayinki na uwar ’ya’ya ki rika cika alkawari kuma ki rika koya wa ’ya’yanki cika alkawari. Misali idan kika tura dauki ya karbo bashi daga makwabta cewa za ki biya gobe, to goben tana yi ki yi kokari ki tura wannan da da biyan bashin da kika karbo, ya san kin cika wannan alkawari. Sannan idan kika ce za ki yi wa danki wani abu na alheri idan ya ci jarrabawa a makaranta, to ki hanzrta cika wannan alkawari, hakan zai sa ya taso da wannan kyakkyawar dabi’a.

Allah Madaukaki Ya ce: “Ku cika alkawari, lallai alkawari abin tambaya ne.” (Isra’i: 34). Kuma Ya ce: “Ya ku wadanda suka yi imani! Ku cika alkawari….” (Ma’ida: 1).

Cika alkawari yana sa mutum ya samu lada mai girma kamar yadda Allah Ya fadi a Suratul Fathi aya ta 10. Kuma da Allah Yake jero wasu siffofin muminai sai Ya hada da masu tsare amana da cika alkawura.

Cika alkawari da mutunta yarjejeniya bai tsaya a tsakanin Musulmi kadai ba, ya hada har da wadanda ba Musulmi ba, hatta kafiran da ake yaki da su, wajibi ne in an yi alkawari ko aka kulla yarjejeniya da su a cika.

Annabi (SAW) ya bayyana yaudara da ha’inci a matsayin siffofin munafukai kamar yadda muka sha ji a cikin Hadisin alamomin munafuki uku ne ko daya Hadisin da ya ce hudu ne. Sannan (SAW) ya ce: “Babu imani ga wanda ba ya da amana, kuma babu addini ga wanda ba ya da alkawari.”

Uwar ’ya’ya muna nusar da ke ce kan wadannan halaye saboda ke ce ruhin al’umma wannan ya sa ake cewa idan aka ba ki ilimi an ba wa al’umma ce ba mutum daya kamar namiji ba. Idan kika gyaru sai ’ya’yanki su gyaru daga nan sai unguwa ta gyaru na gari ma su gyaru har a kai ga kasa.

Allah Ya taimake ki wajen sauke wannan nauyi da ke kanki.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin