Da Dumi Dumi

Gareth Bale na iya zama dan kwallo mafi tsada a duniya

Gareth Bale a lokacin da yake murna jefa kwallo a raga yayin wani wasaAkwai yiwuwar dan wasan kulob din Tottenham da ke Ingila Gareth Bale ya zama mafi tsada a duniya bayan kulob din Real Madrid da ke Sifen ya taya shi Yuro miliyan 100.
Sai dai Shugaban kulob din Tottenham Daniel Leby ya ce idan har Madrid tana son dan wasan sai ta biya Yuro miliyan 145, al’amarin da har yanzu Madrid ba su ce komai ba.
Idan har aka kulob din Tottenham ya amince da tayin Real Madrid, to Gareth Bale zai zama mafi tsada a duniya, inda zai kafa sabon tarihi tun bayan da kulob din Real Madrid ya sayi Cristiano Ronaldo daga Manchester United a kan Yuro miliyan 96 a shekarar 2009.
Tarihi ya nuna a cikin cinikayyar ‘yan kwallo mafiya tsada biyar da a aka yi a fagen kwallon kafa, hudu daga ciki kulob din Madrid ne ya yi su- idan ka cire kulob din PSG da ke kasar Faransa da ya cefano Zlatan Ibrahimobic daga kulob din Inter Milan a kan Yuro miliyan 75.
Real Madrid ta sayi Zinedine Zidane a kan Yuro miliyan 69 sai  Ricardo Kaká a kan Yuro miliyan 65.
“Idan har Madrid suna son Gareth, sai su biya Fam miliyan 125, shi ke nan ya zama nasu. Amma a zahirin gaskiya ba za mu sayar da dan wasanmu ba. Domin kudi ba shi ne komai ba, a’a, a samu dan wasan da zai haskaka maka kulob dinku a rika jin sa a duniya shi ne a kan gaba.” Inji Daniel Leby.
Shin ko Bale zai canza sheka zuwa Madrid? Lokaci ne kawai zai nuna hakan.

Share