✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gareth Bale zai rika karbar albashin Naira miliyan 471 a mako

Rahotanni da ke fitowa daga Sifen sun ce dan kwallon Real Madrid, Gareth Bale ya amince da tayin wani kulob din Jiangsu Suning na kasar…

Rahotanni da ke fitowa daga Sifen sun ce dan kwallon Real Madrid, Gareth Bale ya amince da tayin wani kulob din Jiangsu Suning na kasar China ya yi masa na biyansa albashin Fam miliyan 1 (kimanin Naira miliyan 471) a mako.

Rahoton ya nuna tuni dan kwallon ya amince da wannan tayi kuma akwai yiwuwar ya bar Madrid nan da karshen watan da muke ciki.

Bale wanda ya koma Madrid a 2013 daga kulob din Tottenham ya taimaki kulob din wajen lashe kofunan Zakarun  Turai, sau hudu da kuma wasu kofuna a Sifen.

Idan cinikin ya kullu, zai kasance dan kwallon da ya fi karbar albashi a duk fadin duniya.

A makon jiya ne Kocin Real Madrid Zinedine Zidane ya bayyana Bale a matsayin dan kwallon da kulob din zai sayar kafin a fara kaka ta bana.

Tuni kulob da dama suka shiga zawarcin Bale, ciki har da Jiangsu Suning na China.

Rahotanni sun ce tuni Bale ya amince da tayin, kuma ana sa ran ya koma China nan ba da jimawa ba.