✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gargadin karshe  kan ambaliyar ruwa

Hukumar Kula da Yanayi ta Kasa (NIHSA) ta fitar da sanarwar hasashen samun ambaliyar ruwa a makon jiya, ambaliyar da ake hasashen za ta iya…

Hukumar Kula da Yanayi ta Kasa (NIHSA) ta fitar da sanarwar hasashen samun ambaliyar ruwa a makon jiya, ambaliyar da ake hasashen za ta iya jawo barna mai yawa. Daga cikin bangarorin da ake hasashen samun ambaliyar akwai jihohin Neja da Edo da Abiya da Jigawa da Adamawa da Delta  da Ribas da Kuros Riba da Oyo da Enugu da Kebbi da Nasarawa da Bauchi da kuma Babban Birnin Tarayya, Abuja.

A lokacin da ya ke ganawa da manema labarai a Abuja Daraktan Hukumar NIHSA Injiniya Clement Nze, ya bayyana cewa akwai yiyuwar samun ambaliyar ruwa a dukkan jihohi 36 da ke fadin kasar nan.

Ya ce hukumar ta yi dubi a tsanake a kan sha’anin ambaliyar ruwan da ta faru a baya domin kokarin da kile faruwarta a yanzu. Da yake kare hasashen ambaliyar ruwan ya ce ambaliyar ruwa daga Kogin Neja zai faro ne daga kasashen Guinea da Mali da Nijar da Burkina Faso da Kwaddibuwa da  Benin da Chadi da Kamaru nan da wata guda.

Injiniya Nze ya ce hukumarsu ta yi irin wannan hasashen a shekarun da suka gabata. Amma masu ruwa-da-tsaki a jihohi da daidaikun mutane suka yi biris da gargadinsu. 

Injiniya Nze ya ce, “Rashin daukar gargadinmu da masu ruwa- da-tsaki suka yi ya jawo mummunan sakamako. Rashin daukar mataki ga ambaliyar ruwa, yana haifar da asarar rayuka da dukiyoyi yana lalata gonaki kana ya jawo koma-baya ga tattalin arziki. Saboda haka gwamnatocin jihohi da na kananan hukumomi su tabbatar  duk wani gini da  aka yi shi a kan magudanun ruwa sun cire shi sannan a yashe magudanun ruwa da sauran hanyoyin da ruwa yake bi.”

’Yan Najeriya ba sa daukar matakan kariya. Wannan haka yake lura da irin yadda mutane suke gina gidaje a kan magudanun ruwa ko kuma a gefen kogi. Ko da jami’an da suke da alhakin kula da yanayin da ake bi wajen gina gidaje da sauran gine-gine za ka ga suna ba da hadin kai wajen irin wadannan gurbatattun gine-gine saboda su ma sun fada cikin irin wannan hali. A lokacin da ambaliyar ruwa ta auku tana  rusa gine-gine wadda babu abin da zai tsaida hakan.

Muna kira ga gwamnati cewa wannan hasashen na bana, ya zama darasi, kuma ya bambanta da irin matakan da aka dauka a baya. A wadansu kasashe idan aka samu irin wannan gargadi to gwamnati takan kwashe wadanda suke zaune a wuraren da ake hasashen ambaliyar ruwa ta kai su wasu matsugunnai na daban masu aminci. A Najeriya kuwa akasin haka ne ke faruwa. Mutanen da hadarin zai shafa ana barinsu ne kowa ya yi ta kansa. gonakinsu da gidajensu duk suna salwanta. Ana asarar rayuka da dama kafin Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) ta kai dauki. A wannan karo akwai bukatar gwamnati ta dauki matakin da ya dace na yi shirin tunkarar wannan matsala sosai a bana.

 A cikin shekarar 2012 ambaliyar ruwa ta yi sanadiyyar mutuwar mutum 363 wadda ta fara a cikin watan Yuli sannan ta raba mutum miliyan 2.1 da muhallansu. Kamar yadda Hukumar NEMA ta sanar cewa jihohin Najeriya 30 ne suka samu matsalar ambaliya. Wanda shi ne mafi muni a cikin shekara 40 da suka wuce, inda aka kiyasta cewa mutum miliyan 7 ta rutsa da su sannan ta janyo asarar da aka kiyasta ta kai Naira tiriliyan 2.6.

Shekara bakwai  bayan fa ruwar ambaliyar, mutane har yanzu sun kasa komawa muhallansu na asali lura da cewa har yanzu ba su farfado daga asarar da suka yi ba.

 Har yanzu ana ganin mahukunta a Abuja ba su dauki matakan da suka da ce ba. A baya-bayan nan an samu rushewar wasu muhalli a Unguwar Lokogoma bayan da aka tafka ruwa kamar da bakin kwarya na wasu sa’o’i masu yawa. Wannan ba shi ne karo na farko ba da ake samun asarar rayuka da dokiyoyi a Birnin Tarayya ba. Amma har yanzu mahukunta suna yin ko-in-kula da irin hadarurrukan da suka faru a baya. Suna farkawa ne kawai idan wani hadari ya auku.  Ambaliyar da ta auku a yankin Lokogoma da ke Abuja ’yan kwanakin nan ta yi sanadiyyar mutuwar Daraktan Babban Kotun Tarraya da ke Abuja Mista Tony Okecheme. Yankin da Daraktan ya mutu an bayyana shi a matsayin yanki mai hadari ga direbobi da mazauna yankin tun lokacin da ake aikin gina gada a shataletalen Galadimawa. Amma babu wata alama da za ta nuna cewa akwai hadari a kusa, don haka kowa na iya fadawa cikin tafki wanda zai cutar da shi nan take. 

Haka abin yake a sauran sassa daban-daban na jihohin kasar nan yayin da mutane suke zaune cikin tsoro. A bara akalla mutum 100 sun rasa rayukansu a cikin jihohi 10. A Jihar Neja kadai sama da mutum dubu 10, suka rasa mahallinsu a ambaliyar ruwan da ta auku a  kananan hukumomi  23 daga cikin 25 da jihar ke da su. Masu iya magana dai sun ce rigakafi ya fi magani.