✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Garkuwa da mutane: Gobara daga kogi! (2)

Wannan hali na hadama da son samun komai a cikin gaggawa da kuma tara abin duniya ta kowane hali, ya shafi kowane bangare na rayuwarmu…

Wannan hali na hadama da son samun komai a cikin gaggawa da kuma tara abin duniya ta kowane hali, ya shafi kowane bangare na rayuwarmu ya shafi kusan kowa da kowa. Don haka ne kafin a magance sata da garkuwa da mutane wajibi ne a tuttuge wannan muguwar dabi’a ta son tara abin duniya da mugunta da hadama tun daga tushe.

Garkuwa da mutane tana matukar gurgunta harkokin rayuwa da tattalin arziki musamman a nan jihohin Arewa wadanda ba wasu masana’antun kirki muke da su ba, illa noma da kiwo da harkar kasuwanci. Kuma abin takaici wadannan sana’o’i biyu da kasuwancin suna neman rugujewa saboda ayyukan wadannan miyagu daga cikinmu. Domin a yanzu haka mutane da dama sun sallamar da harkar noma ko kiwo a akasarin wuraren da masu garkuwa da mutanen suke kai hari. Kuma mutane da dama sun hakura da harkar kasuwanci daga wannan gari zuwa wancan a tsakanin jihohin da lamarin ya fi kamari.

Bari in kawo misalan abubuwan da suka faru da wadansu daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su, wadanda na sansu ko na san na kusa da su, kuma lamarin ya sanya suka daina noma ko gudanar da harkokin kasuwancin da suka saba.

Akwai wani makwabcinmu da muka zauna tare da shi a garin Kaduna wanda yake da gona a kusa da kauyen Barakallahu a kusa da Kasuwar Duniya ta Kaduna kuma kusa da garin Rigacikum da ke Karamar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna, wannan bawan Allah ya je gewayar gonarsa a wata Juma’a jim kadan bayan idar da Sallar Juma’a. Yana zuwa gonar sai ya shiga zagayawa amma bai ga masu gadin gonar ba, ya ci gaba da zagayawa kwatsam sai ya ga mutane da bindigogi sun kewaye shi suka kama shi suka ce sun yi garkuwa da shi suka bukaci ya kawo Naira miliyan 30, in yana so a sake shi. Lokacin da ake tattaunawa da masu garkuwa da shi, matar wannan bawan ta rika ba su hakuri kan su rage kudin, amma abin mamaki sai suka shaida mata cewa ai da ma ita suka kama, domin sun samu labarin danginta suna da kudi. Sannan suka ce me zai hana su sayar da gidan mijin nata da ke wuri kaza! A karshe sai dai aka biya su Naira miliyan uku kafin su sako wannan mutum wanda tun daga ranar ya yi ban kwana da wannan gona tasa. Kuma abin mamaki ya ce a lokacin da aka biya kudin masu garkuwa da shi da suka yi masa rakiya zuwa bakin hanya sai ya rika jin daya daga cikinsu yana cewa, shi fa ba zai yarda ba, yaya za su kama wannan bawan Allah wanda daga gani mutum ne mai addini mai mutunci a karbi Naira miliyan uku, amma a ce Naira dubu takwas-takwas kawai za a biya su. Ya rika nanata wa abokan harkarsa da suke rakiyar tare cewa shi fa ba zai yarda ba. Wannan makwabci namu yanzu dai shi da gonar sun yi ban kwana.

Na biyu lokacin da aka tarwatsa masu garkuwa da mutane a jihohin Zamfara da Katsina da Kaduna, wadanda suka koma yankin Bauchi sun mamayi dajin kauyukanmu a yankin Toro, kuma abin takaici suna zuwa sai aka ji daya yana cewa ‘shege wane ashe nan ya dawo?’ Cikin ’yan kwanakin kadan sai suka sace ’yarsa suka nemi makudan kudi. Haka Bafulatanin nan ya rika jigilar shanu zuwa Jos yana sayarwa don samar da kudin da suka nema.

Kuma sakamakon ta’asar masu garkuwa da mutanen, Fulanin da suke zaune a Arewacin Gundumar Zaranda a Karamar Hukumar Toro, Jihar Bauchi, musamman dajin ’Yuga, tilas daruruwansu suka yi gudun hijira. Ga mai bin hanyar Jos zuwa Bauchi a kai-a-kai zai yi wahala a ce bai hadu da dandazon Fulani a garin Nabordo ba a kan hanyarsu ta yi hijira daga yankin a shekara uku zuwa hudu da suka gabata ba.

Abin takaici a lokacin wannan harka ta garkuwa da mutane ta shiga yankin sai ga ’ya’yan Fulanin yankin su shige ta sosai, ta yadda aka rika samun dan kane ko dan wa yana hada baki da wadansu a zo a kama wa ko kanen mahaifinsa don a karbi kudin fansa su raba! Ba a samu sa’ida a yankin ba, sai da aka samu wata kungiya mai suna ‘Ba Beli’ wadda ta samo asali daga Karamar Hukumar Ganjuwa a jihar ta rika bi tana kashe barayin shanu da masu garkuwa da mutanen da ba su mika wuya ba.

Sannan kasa da mako biyu da sako wani abokin aikinmu wanda aka kama shi tare da wadansu mutum takwas a kusa da kauyen Rinjana da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna inda suka shafe kwana takwas, sai ga shi a ranar Talatar makon jiya an sake kama matafiya su takwas ciki har da ’yan kasuwa a daidai wurin da aka kama su a kusa da Rijana. Cikin mutanen da aka yi garkuwa da su har da wani mai sana’ar dinki da ya koma saye da sayar da haja a kauyen Gidan Busa da ke hanyar Abuja zuwa Kaduna wada ya koma kauyen da zama daga Abuja a shekraun baya.

Wani dan uwan wanda aka kama din ya ce daga farko an nemi su biya Naira miliyan daya, kuma suna cikin kama wannan sayar don a samu a tara abin da za a iya, sai wani daga cikin masu garkuwar, ya ce cinikin ma ya tashi ya koma Naira miliyan biyu, saboda su ma sarinsu suka yi! A karshe dai bayan an kai an kawo sai wani daga cikin masu satar mutanen ya yanke cewa a kawo Naira dubu 500 idan kuma ba haka ba, za su kashe shi suna da wadanda suke bukatar sassan jikin mutum da za su saya! Haka aka kukuta aka biya wannan kudi kafin a sako shi a ranar Lahadin da ta gabata. Kuma babban abin takaici da ban haushi kudin fansar wannan bawan Allah an biya su ne a bayan wani gidan mai a kusa da Unguwar Kawo da ke garin Kaduna, inda aka shaida wa masu biyan cewa su je Rijana su dauki dan uwansu nan da wani lokaci.

Yadda aka mayar da mutane tamkar shanu ko tumaki ana cinikinsu bayan an sace su abu ne marar dadi, musamman idan mutum ya ji irin ukubar da masu garkuwa da mutanen suke jefa jama’a a ciki, da niyyar takura wa iyalan wadanda suka kama su sayar da duk abin da suka mallaka don fanso dan uwansu.

Babban abin takaici kuma shi ne a yayin da hukumomin tsaro suke bakin kokarinsu yi don magance wannan muguwar annoba da take barazana ga rayuwa da tattalin arziki, kuma take neman jawo wata annobar ta hanyar tilasta jama’a suna sayen bindigogi da sunan kare kai da kuma wadanda suke zuwa wurin masu da’awar suna da maganin bindiga don saye da sunan kariya, a gefe guda kuma akwai korafe-korafe da zarge-zarge cewa masu garkuwa da mutanen suna baje kolinsu yadda suka ga dama ne sakamakon hadin baki da wadansu baragurbin ma’aikatan tsaro musamman ’yan sanda.

Ana zargin cewa akwai baragurbin ’yan sanda da wadansu jami’an tsaro da suke hada baki da masu garkuwa da mutanen wadanda ake zargin suna kawo musu wani kaso daga kudin da suka tatsa daga jama’a. Kai akwai ma zargin cewa wani lokac ’yan sanda da jami’an tsaro ne suke sayo wa masu garkuwa da mutanen harsasan da suke amfani da su wajen barazana da firgita mutanen da suke kamawa suna yin garkuwa da su. Lallai biri ya yi kama da mutum game da zargin hannun baragurbin jami’an tsaro a harkar garkuwa da mutane in ba haka ba, yaya duk da dimbin jami’an tsaron da suke kan hanyar Kaduna zuwa Abuja, amma a ce kusan kullum sai an sace mutane an shiga da su cikin daji? Me ya sa ake auka wa mutanen a yi garkuwa da su a kusa da inda ’yan sanda suke? Ina wadanda aka kama bisa zargin garkuwa da mutane suke? An gurfanar da su a gaban kotu ko kawai an je an tsare su ne ko ma an sake su sun koma fagen fama? Yaya batun zargin da ake yi cewa da dama daga cikin ’yan sandan da suke aiki a tsakanin Katari zuwa Rijana ko an yi musu canjin wurin aiki sukan koma wurin da aiki?