Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Garkuwa da mutane: Gobara daga kogi! (3)

Sufeto Janar Mohammed A. Adamu

Bayan mun yi rubutu sau biyu kan matsalar garkuwa da mutane da ta zama alakakai kuma ruwan dare a jihohin da dama kuma ta fi ta’azarra a jihohin Zamfara da Katsina da Kaduna da Kogi da Babban Birnin Tarayya, Abuja,  yau za mu waiwayi bangaren jami’an tsaro ne.

Hakika akwai zarge-zarge da dama da ake yi cewa baragurbin ’yan sanda da wadansu jami’an tsaro suna hada baki da masu garkuwa da mutane, tare da daure musu gindi suna aikata wannan muguwar ta’asa, saboda dan abin duniya da suke samu. Kuma ana zargin wadannan ’yan sanda da jami’an tsaro da samar da bindigogi wani lokacin haya da harsasai ga masu garkuwa da mutanen da sauran ’yan bindiga.

ADVERTISEMENT

Duk lokacin da na ji irin wannan zargi nakan tuno ne da Lawrence Anini wani kasungurmin dan fashi da makami da zakararsa ya yi cara a zamanin mulkin Janar Ibrahim Babangida a shekarun 1990. Wannan dan fashi da ayarinsa sun tayar da hankali a kasar nan, a karshe an iske cewa hadin kan da ya samu daga ’yan sanda ne ya sa ya zama barazana a kasa baki daya. Ya zama kamar aljani da babu mai son jin sunansa. Ashe-ashe, kwamandan ’yan sanda masu yaki da fashi da makami a tsohuwar Jihar Bendel, George Iyamu ne babban mai daure masa gindi, inda da asiri ya tuno Anini ya ce har zuwa wurinsa yake yi ya ba shi kudi kafin ya fita fashi da makami ya samo musu!

A lokuta da dama idan mutum ya ga yadda masu garkuwa da mutane suke cin karensu babu babbaka, in aka ce masa akwai hannun jami’an tsaro musamman ’yan sanda dole ya yarda. Misali wata majiya ta ce lokacin da tsohon Sufeto Janar Ibrahim K. Idris ya ziyarci kauyen Rijana da ke hanyar Abuja zuwa Kaduna ya bukaci mutanen kauyen su rika taimaka wa ’yan sanda da bayanan da za su sa a rika kama masu garkuwa da mutanen. Amma sai basaraken kauyen ya shaida masa cewa ba za su iya ba, saboda mutum daidai har 18 aka kashe a kauyen bayan sun kai rahoton wadanda ake zargi da garkuwa da mutanen ga ’yan sanda!

ADVERTISEMENT

Shin wa ya gaya wa masu garkuwa da mutanen cewa ga wadanda suka kai rahotonsu har aka bi su aka kashe? Wannan abu ne da babu wanda za a zarga sai ’yan sandan da aka kai wa rahoto. Ke nan idan har zan kai rahoto ga ’yan sanda ina zargin wane yana cikin masu aikata barna kaza bayan kwana biyu a iske gawata an kashe ni, yaya za a yi wani ya kara kai rahoton wani da ya gani yana aikata ta’asa?

Na biyu a wannan hanya ta Abuja zuwa Kaduna a tsakanin kauyukan Katari zuwa Rijana, wani direba da zai tafi Kano a ’yan watannin baya, ’yan sandan sun tsare shi suka ce ya dauki wani Bafulatani zuwa wani wuri a gaba kadan, to ganin shi mai doguwar tafiya ce da bai son tsaye-tsaye, sai ya ce babu wuri a cikin motar, sai wani dan sandan ya ce da shi. “To kuwa za ka yi ta ranka.” Jin haka sai fasinjojin motar suka ce da direban ya dauke shi. Bayan ya dauke shi, suna cikin tafiya sai Bafulatanin ya ce ko kuna tsoron ni mai garkuwa da mutane ne? Ya ce, shi din ne yanzu ma ya kawo wa ’yan sandan nasu kaso ne na Naira dubu 400!  Kuma ana zuwa daidai inda aka ce a kai shi, sai ga wata sabuwar mota kirar Toyota Hilud ta zo ta dauke shi sun yi cikin daji!

Idan mutum yana hira da direbobin da suke bin hanyar Kaduna zuwa Abuja zai rika jin labarai na ban takaici game da halayyar jami’an tsaro, musamman ’yan sandan da suke aiki a yankin, wadanda suke zaune a wurin ko wadanda aka tura su aiki na wucin-gadi.

Akwai direban da ya taba shaida wa wata majiya cewa, ya taba zuwa ya iske ’yan bindiga sun tsare hanya a kusa da inda jami’an tsaro suke, ya juyo ya shaida wa ’yan sandan cewa can gaba ana fashi, amma a cewarsa budar bakin wani dan sandan cewa ya yi ai gara ’yan fashi da ku, su da za su iya ba mu Naira dubu 10 ku kuwa fa?

Sannan an rika zargin cewa akwai ’yan sandan da ko an yi musu sauyin wurin aiki daga yanki za su je su yi kamun kafa in ta kama ma su biya kudi a dawo da su, wani ya ba ni misali da wata jami’ar ’yan sanda da aka ce sau biyar ana yi mata sauyin wurin aiki daga yankin, amma sau biyar tana komawa.

Sannan abokin aikinmu Ahmad Garba da aka kama a ranar 7 ga Maris din bana a hanyar Abuja zuwa Kaduna a kusa da kauyen Rijana, ya ce lokacin da ake tattaunawa kan kudin fansarsa, sai suka ga an kawo wa masu garkuwa da su fakiti uku na harsasai, kuma suka ce musu, “Kun gani ko, wadannan bindigogi da harsasai mu muke kerawa a nan?” Suka ce ba su suke kerawa ba kawo musu ake yi kuma masu kawo musu jami’an tsaro ne, don haka a cikin kudin fansarsu akwai nasu kason shi ya sa suke tsanantawa kan kudin fansar.

A kauyen Gidan Busa da ke wannan hanya dai an taba samun yunkuri daga maharba da ’yan tauri, inda suka shiga dajin da ’yan bindigar suke suka yi artabu da su, aka kashe mutane daga bangarorin biyu. A cewar mutanen kauyen cikin gawarwakin wadanda ake zargi ’yan bindigar ne har da wani babban dan sandan yankin da ya yi shigar Fulani. Kuma da aka nuna wa na gaba da shi, sai ya ce wai ba san jami’in yana wannan aiki ba.

Wa ya san bayanan da za a bayar game da wannan dan sanda? Kila a ce ya mutu ne lokacin da ’yan sanda suka je fafatawa da ’yan bindiga, alhali ba haka ba ne. Kuma alamar hakan ta bayyana lokacin da ’yan sandan suka koma farautar ’yan tauri da mafarautan da suka kai harin suna kokarin kama su lamarin da ya sa jagoran ’yan tauri da mafarautan ya gudu daga kauyen na Gidan Busa.

Kamar yadda na fadi irin wadannan labarai marasa dadin ji suna da yawa a hanyar Kaduna zuwa Abuja, kuma ga dukkan alamu hakan ne ya sa masu garkuwa da mutane da sauran ayyukan ta’asa suke baje kolinsu a yankin. Kuma abin takaici duk lokacin da aka sace mutane idan aka tuntubi hedkwatar ’yan sandan Jihar Kaduna, maimakon su tsananta bincike a kai, sai kawai su ce karya ake yi, idan kuma akwai shaidar da ta nuna abin ya faru sai su ce ana kara gishiri a kai, kamar yadda suka rika fadi a makon jiya kafin Gwamna Nasir El-Rufa’i ya ga lamarin da idonsa. Ba don taimakon Allah da Ya kawo Gwamna El-Rufa’i ba, haka za a ci gaba da sace mutane, ’yan sanda kuma suna karyatawa ko su nuna abin da ya faru bai kai ya kawo ba!

Na jero wadannan bayanai ne domin ba hukumomin tsaro na kasar nan haske don su bincika. Bincike na sirri ne kawai zai gano gaskiyar wadannan zarge-zarge tare da samar da maslaha ga wannan muguwar ta’asa da take kassara Arewa a fagen tattalin arziki da zamantakewa da walwala. Idan har hukumomin tsaro ba su tashi tsaye sun yi bincike na sirri ba, to miyagun jami’an tsaro za su ci gaba da daure wa miyagun mutane gindi su ci gaba da aikata wannan muguwar ta’asa da sauran miyagun ayyukan da ba a san illar da za su yi wa kasar nan ba nan gaba.

Wannan kalubale ne ga Mukaddashin Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya Mohammed Adamu da Shugaban Hukumar Tsaron Kasa (DSS) Alhaji Yusuf Magaji Bichi da Babban Mashawarcin Shugaban Kasa kan Tsaro, Manjo Janar Babagana Mongono da sauran wadanda alhakin tsaron kasa yake hannunsu.