✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Garkuwa da mutane: Matsin ’yan sanda ya sa Fulani kaura daga Rijana

Al’ummar Fulani mazauna garin Rijana da ke kan hanyar Kaduna zuwa Abuja sun fara kaurace wa garin sakamakon abin da suka kira kama su da…

Al’ummar Fulani mazauna garin Rijana da ke kan hanyar Kaduna zuwa Abuja sun fara kaurace wa garin sakamakon abin da suka kira kama su da jami’an tsaro da ke aikin kawar da masu garkuwa da mutane suke yi a yankin.

Aminiya ta gano akasarin Fulanin da ke garin Rijana suna cikin damuwa da tsaro wanda hakan ya sa da dama daga cikinsu ke shirin barin garin zuwa wasu garuruwa.

Tsohon Ardon Gundumar Doka da ke Rijana Alhaji Yahaya Suleiman wanda ya tabbatar da haka a tattaunawarsa da Aminiya, ya ce Fulani mazauna Rijana suna cikin damuwa sakamakon kama su da ’yan sanda suke yi.

Ardon ya ce ’yan sandan da ke aikin tabbatar da tsaro a garin da kewaye na kama Fulanin da ba su ji ba, ba su gani ba, su tafi da su a tsare da sunan masu laifi.

Ya ce, a matsayinsa na daya daga cikin shugabannin Fulanin yankin ba za su taba yarda su boye Fulanin da suka san suna da mugun hali ba.

Ardon ya ce suna goyon bayan yaki da ’yan ta’adda da gwamnati ke yi a hanyar Kaduna zuwa Abuja, amma suna kira a rika bambanta batagari da na kirki a cikin al’ummar Fulanin da ke zaune a garin. “Gaskiya muna jin dadin matakan da gwamnati ke dauka domin inganta tsaro a wannan hanya, hakan ya sa muke yin kira ga Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i ya ci gaba da sa ido kan wannan hanya domin a kawar da batagari. Sai dai babban abin da ke damunmu shi ne yadda jami’an tsaron da aka turo aiki ke shigowa cikin kasuwa da rana suna kama Fulani ba tare da sun fada mana dalilin hakan ba. Babu yadda za a ce a dukkan gari ba na kirki. Muna da mutanen kirki a cikinmu wadanda ba su da hannu a abubuwan da ke faruwa amma kuma jami’an tsaro sai su rika kama su,” inji shi.

Ya ce, “Ba muna neman hana gwamnati kama batagari ba ne a cikinmu amma abin da muke cewa shi ne a rika tantance mutanen kirki daga batagari. Mu ba za mu taba goyon bayan mugu ba, kuma muna fatan Allah Ya kawo karshen wannan abu da ke samun jama’armu. Gaskiya ba mu jin dadin yadda ’yan sandan SARS ke kama mutanenmu ba, wanda hakan ya sa mutanenmu ke neman barin gari.”

“Duk wanda ya aikata laifi a kama shi kuma ba za mu je ba amma na kirkin a rika tantace su. Muna kira ga Gwamna El-Rufa’i ya dubi wannan matsala da muke fama da ita ta hanyar jan kunnen jami’an tsaro su rika tantance na kirki daga mugu. A shirye muke mu taimaka wa jami’an saro amma duk abin da za su yi a yi shi bisa kaida,” inji shi.

Ya ce kwana uku ke nan da jami’an tsaro suka kama wadansu mutanensu uku a kasuwa kuma a ranar Lahadi ’yan sanda sun sake kama wadansu Fulani hudu a hanyarsu ta zuwa kasuwa. “Kamar yadda na ce a iya saninmu ba su da wani mugun hali, saboda idan har suna da wani mugum hali ba za mu bata lokacinmu wajen zuwa neman a sake su ba,” iji shi.

Shugaban Matasan Fulanin Rijana, Yakubu Baushe ya nuna rashin jin dadinsa kan abin da ke faruwa da ’yan uwansu. Ya ce hakika suna bai wa jami’an tsaro goyon baya amma yadda ake kama Fulani abin na damunsu. “Gaskiya idan abin da ke faruwa a Rijana ya ci gaba jami’an tsaro za su tarwatsa mutanenmu daga garin wannan shi ne abin da ke damunmu a yanzu. Abin ya yi muni har ta kai ga ’yan sanda na fito da mutanenmu daga cikin motar haya a tsare su ba tare da sun aikata wani laifi ba,” inji shi.

Ya ce, “Ba su ma tambayar mutum aiki ko sana’ar da yake yi sai dai su kama su tsare. Mu Fulani muna cikin wani yanayi na damuwa a hannun jami’an tsaro. Muna kira ga gwamnati ta kawo mana dauki domin a yanzu muna cikin damuwa.”

Sarkin Hausawan Yamma a Rijana, Alhaji Rabi’u Abdullahi ya ce suna zaune lafiya da Fulanin garin Rijana amma ya yaba wa gwamnatin a kan matakan da take dauka a hanyar Kaduna zuwa Abuja inda ya ce matakan sun taimaka sosai wajen rage garkuwa da mutane da ake yi a hanyar. “Tun daga waccan Lahadin ba mu sake jin an tare wata mota a kan wannan hanya ba, saboda jami’an tsaro na kan hanyar kuma mun ji an ce akwai shirin kafa sansanin soji a kan hanyar,” inji shi.

Ya ce “Gaskiya a kwanakin baya mutane sun kaurace wa zuwa gonakinsu a yankin domin tsoro. Saboda a baya idan sun je gona mutanen na koro su daga dajin amma yanzu an samu canji, mutane na zuwa daji saboda jami’an tsaro na aiki a dajin.”

“Masu zuwa hakar ma’adinai ma sun shiga dajin sun dawo suna fada mana cewa wadannan mutane (masu garkuwa) sun fice. Da wannan muke mika godiyarmu ga hukuma bisa wannan aiki da suke yi domin zaunar da mu lafiya,” inji shi.

Sarkin Kasuwar Rijana, Tasi’u Lawal ya ce a makonnin baya hanyar Kaduna zuwa Abuja ba ta biyuwa amma yanzu an samu sauki. Ya ce lokacin daga karfe shida zuwa bakwai na yamma ababen hawa ke kaurace wa hanyar amma yanzu an dan samu sauki.

“Yanzu mutanenmu na zuwa gonaki saboda haka muna kira ga gwamnati ta ci gaba da aikin da take yi a kan hanyar domin a samu sauki. Allah Ya kawo mana sauKi,” inji shi.

Dagacin Fadan Achi da ke Rijana, Mista Ayuba Dodo Dakolo kira ya yi da al’ummar Fulani su tabbatar sun bayyana duk wani bako da ke cikinsu domin kauce wa saukar da mai mugun hali a gidajensu.

Da wakilinmu ya tuntubi Kakakin ’Yan sandan Kaduna DSP Yakubu Sabo kan wannan zargi ya  aiko masa sakon cewa yana halartar taro zai kira amma har hada wannan rahoto bai kira ba.