Search
Subscribe
Garkuwa da mutane: Muna tsananin bukatar addu’ar ‘yan uwa

Garkuwa da mutane: Muna tsananin bukatar addu’ar ‘yan uwa

Assalam Editan wannan jaridar tamu mai albarka wato jaridar Aminiya, da fatan dukan ma’aikata da abokan arziki suna cikin koshin lafiya amin. Ina so  ka dan ba ni fili in yi tsokaci a kan bai wa masu garkuwa da mutane kudi da cewa wata fitina ce da ta fi garkuwar hadari. Al’umma mu dukufa da addu’o’i, domin su suka fi komai muhimmanci a yanzu, da wannan muna matukar bukatar haka.

Jarrabawar da babban malami Alaramma Ahmad Sulaiman ya fada a ciki da abokan tafiyarsa, jarrabawa ce mai girma a wurinmu. Kuma alhamdulillahi da Allah Ya kubutar da su.

Bai wa ’yan ta’addan nan kudi a irin wannan lokaci, ba karamar fitina ba ce aka bude, domin kudin fansar na taimakon masu garkuwar matuka.

Addu’a muka fi bukata fiye da komai. Allah Ya tona asirinsu.

Daga Saminu Artillery Yelwa Shendam Jihar Filato: 08032436477 e-mai:saminuartillery1@gmail.com

Addu’a ga Ahmed Garba

Salam Editan AMINIYA mai albarka. Ina so ka taimake ni in isar da sakona ga Malam Ahmed Garba Muhammed da fatan Allah Ya kiyaye gaba kuma Allah Ya mayar masa da alheri, mu ma matafiya Allah Ya kare mu a ko’ina Allah Ya raba mu da wadannan mutane amin.

Daga Alhaji Jinjiri Na Alhaji Shu’aibu Mile 12 Legas 09023489162.

 

Kan zaben Kano

Assalam Edita, zaben Kano da aka gudanar ’ya nuna dimokuradiyyar Najeriya na bukatar garambawul da zai kara tabbatar da cewar dimokuradiyya ta samu gindin zama, ba wai wanda zai kawo wa dimokuradiyyar Najeriya tawaya ba.

Daga A.U Shuwaki, 08063511757.

 

Rahoton garkuwa da Ahmed Garba ya sani hawaye

Assalam Edita, ina so ka ba ni dama in taya dan uwana da masu garkuwa da mutane suka sako Malam Ahmed Garba. Karanta labarin ya sa na zub da hawaye. Ubanjigi Allah Ya ba ka lafiya duk wanda ya taimaka har ka dawo Allah Ya saka musu da Aljanna, amin,

Umar Kano Sarkin Yakin Dausayin Kauna FDK Aminiya, 07035438533

Jinjina ga Kanawan Dabo

AMINIYA muna jinjina wa Kanawan Dabo da suka sake zaben Gwamna Abdullahi Umar Ganduje. Godiya ta musamman ga Abdullahi Abbas Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Kano da Nasiru Gawuna da gwarzon shekarar bana Murtala Sule Garo. Allah Ya ba ku ikon adalci.

Daga Hon. Aliyu Abba PRP 08136731410.

 

Jaje ga Musulmin New Zealand

Assalam Editan Aminiya.  Ka isar da jajena da ta’aziyya zuwa ga Musulmi da sauran jama’ar kasar New Zealand bisa ga mummunan kisan gillar da wani dan ta’adda ya yi wa Musulmi a masallatai biyu na Juma’a. Wannan aika-aikar ta bakanta wa jama’ar Musulmi rai ainun. Muna addu’a Allah Ya gafarta wa wadannan bayin Allah, Ya ba ’yan uwansu hakuri. Kasar Amurka da Turawan Yamma yanzu su sani ba Musulmi ne kurum ’yan ta’adda ba. Da fatan Allah Ya yi mana kariya daga miyagun mutane masu yi wa Musulmi hassada, amin.

Daga Abdullahi Zauro Jihar Kebbi 08069077363.

 

Sakon taya murna ga Gwamna Ganduje

Salam. Don Allah Edita ka ba ni dama in mika sakon taya murna da fatan alheri ga zabbben Gwamnan Kano a karo na biyu wato Dokta Abdullahi Umar Ganduje. Ina addu’ar Allah Ya taya shi sauke wannan nauyi. Allah Ya yi riko da hannayensa, kuma da fatan ba zai manta da irin halaccin da mutanen karkara suka yi masa ba wajen saka alheri da alheri.

Daga Shehu Mansur Sule, Getso Jihar Kano 08037520051.

 

Zaben Kano zubar da kimar jama’ar Arewa ne

Ina rokon Editan jaridar Aminiya ka ba ni dama domin in bayyana ra’ayina game da zaben da aka ce Ganduje ne ya ci. A gaskiya wannan abin kunya ne ga ci gaban dimokuradiyya da Jihar Kano da Arewa da kasa baki daya. Muna fatan Allah Ya kawo mana masu kishin kasa da son gyara na gaskiya ba na yaudara ba, amin summa amin.

Daga Aminin Aminiya Sani CK, Karamar Hukumar Madobi, Jihar Kano 08061600962.

 

Kannywood: Zango ya yi gaskiya

Assalam. Ina so in yi karin bayani kan maganar Adam Zango, gaskiya ce abin da ya fada kowace kungiya ko runduna idan babu hadin kai da son juna da tausayi da taimakekeniya, to ci gaba ba zai samu ba. Kalli abin da ya faru da Shu’aibu Nabodara, abin tausayi ne, irin su an ci moriyar ganga an yada kwaurenta. Ina su Zainab Indomi. Duniya ina za ki damu? amma tambaya ita ce ba dattawa a Kannywood ne? Ni a nawa ganin son abin duniya da hassada ya kawo halin da ake ciki idan ko za a ci gaba da tafiya a haka Kannywood za ta zama tarihi. Shawara gare ku ku zauna ku nemo bakin zaren.

Daga Alkasim Yola 09068389953.

 

Ta’aziyya ga iyalan Rabi’u Ar-Rahuz

Salam Edita, ina son a mika min ta’aziyyata ga iyalan Rabi’u Haruna Ar-Rahuz babban dan kasuwa kuma furodusa wanda ya rasu ranar Juma’a sakamakon jinyar da ya yi fama da ita. Allah Ya yi masa rahama Ya ba ’yan uwa hakurin rashinsa da suka yi, amin.

Daga 08139039308.

 

Kira ga gwamnatin Kebbi

Salam Edita. Ka ba ni dama in yi kira ga gwamnati Jihar Kebbi mai albarka ta kara bai wa fannin lafiya muhimmanci sosai ga marasa karfi.

Daga Mansir Dan Alhaji 07032289946.

 

Shawara ga Malam Mai Rusau

Assalamu alaikum. Alhamdulillahi Allah Ya sa ka koma Malam Mai Rusau. To, ina ba ka shawara, ka kalli baya da abin da yake gabanka, tare da damarka da hagunka. Ka yi nazari a kai.

Daga Isah Murtala Gama-gira 08135419744.

 

Kira ga kungiyoyin kare dimokuradiyya

Zuwa ga jaridar Aminiya. Ina so ku ba ni dama in isar da sakona ga kungiyoyin rajin kare dimokuradiyya a Najeriya, sun bar tsarin yayata magudin zabe tun lokacin zaben fid da gwani da aka yi amfani da kudi da karfi da ’yan daba don a ci zaben dole, ba zabin talakaba!

Daga Suleiman Adam Kafardau 07017846306.

 

Taya murna ga Kauran Bauchi

Assalamu alaikum jaridar Aminiya mai farin jini. Ina so ku mika min sakon taya murna ga zababben Gwamnanmu na Jihar Bauchi Sanata Bala Mohammed Kauran Bauchi, ina fatan insha Allah za ka kawo mana canji mai amfani saboda shekara hudu da jihar ta yi hanun wannan gwamnati ba wani abu na ci gaba, ba aikin yi, kasuwanci ya tsaya, ba wuta ba ruwan sha, ba hanyoyi masu kyau, asibitoci ba gyara makarantu abin ya wuce duk tunanin dan Adam. Alhamdulillah da Allah Ya kawo mana canji. Daga karshe ina addu’a Allah Ya taya ka riko don Allah ka tausaya wa al’ummar Bauchi.

Daga Abdullahi Dibo Jama’are 08132428869.

 

Taya murna ga Buhari da Gandue

Salam Edita. Ka ba ni fili in mika sakon taya murna ga Mai girma Shugaban Kasa da Gwamnan Kano. Allah Ya sa su gama mulki lafiya, kuma Ya ba su ikon taimaka wa talakawa amin.

Daga Bello Tata Tudun Wazirci, Kano 08129943809.

 

Magudin zabe: PDP ta tafi APC ta karba

Ana murna PDP ta mutu an daina magudin zabe a Najeriya, ita kuma Jam’iyyar APC ta karba. Ba komai ya sa na fadi haka sai dai yadda na ga APC tana son lashe wasu jihohin Najeriya da karfin tuwo alhali al’umma PDP suka zaba.

Daga Abdoul Abdulhamid, Jihar Zamfara 08167515363.

 

Muna maraba da sabon albashi

Muna maraba da amincewa da sabon tsarin albashi na Naira dubu 30 ga ma’aikata da majalisun dokokin Najeriya suka yi. Tabbas hakan abin farin ciki ne ga ma’aikata, musamman na Gwamnatin Tarayya. Muna kira ga gwamnonin jihohi su rage rayuwa mai tsada da kwasar mukarrabbai barkatai, ta yadda za su samu damar iya biyan wannan sabon albashi. Duk Gwamnan da ya san ba zai iya biya ba, to kamata ya yi kawai ya yi murabus.

Daga Mahmud Salihu Kauran Namoda, Zamfara. 09079551996.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin