Da Dumi Dumi

Gasar BBC-Hausa: Tsokaci da sharhi game da hikayar mata

A wannan makon, GIZAGO (08065576011) ya bugi jaki sannan ya bugi taiki dangane da shahararriyar gasar rubutun kirkirarrun gajerun labarai da Sashen Hausa na Gidan Rediyon BBC ke gabatarwa duk shekara ga mata. Musamman a wannan sharhi da tsokaci, an maida hankali ne kan wasu shawarwari da aka hango, wadanda za su taimaki gasar da ma al’umma idan aka dauki matakan gyarawa:

Kamar yadda ya saba, a wannan karon ma Sashen Hausa na Gidan Rediyon BBC ya sake dawowa da GASAR HIKAYATA, inda yake bude kofa ga marubuta mata su rubuta kirkirarrun labarai da suka danganci rayuwar yau da kullum da ke faruwa ko suka faru a cikin al’ummarsu. BBC ya fara wannan gasa a shekarar 2016.

Ga duk mai kishin Adabin Hausa, ya zama dole ya yaba wa wannan babban yunkuri na BBC Hausa, musamman yadda ya ba da dama ga marubuta musamman mata wajen bayyana tunaninsu, wanda haka kan kara fadada ilimi, taskace tarihi da kuma sassaita al’amuran yau da kullum na al’ummar duniyar Hausawa.

Sai dai wani hanzari ba gudu ba, a matsayina na Editan Adabin Hausa, na rika bibiyar kai-komo na yadda gasar ke gudana, inda na ankara da cewa tun daga fara wannan gasa shekaru uku da suka gabata, an yi ta samun korafe-korafe daban-daban daga mabambantan rukunnan mutane da suka hada da marubutan Hausa maza da masana harkokin addinin Musulunci da ma masu sharhi kan adabin Hausa.

Ta fuskar marubutan kirkirarrun labarai daga cikin maza, wasu daga cikinsu sun yi ta kumfar baki, suna korafin cewa saboda me babban gidan rediyon duniya kamar BBC Hausa zai nuna masu wariyar jinsi? Yaushe zai fito da babbar gasar da ta shafi ilimi, fikira, kirkira amma ya zab’i MATA kadai, ya hana MAZA shiga a fafata da su? A ganin irin wadannan marubuta maza, duniya gaba dayanta tana tafiya ne bisa cudedeniya tsakanin maza da mata, don haka duk wani abu da za a yi, musamman ma da ya shafi harkar ilimi da fad’akarwa, ya zama wajibi a bugi jaki tare da taikinsa – idan an ba mata dama, to su ma maza ya kamata a ba su tasu damar. Don haka, suna ganin cewa ya kamata a ce wannan gasa an bude ta ga maza da mata, kowa ya nuna tasa fasahar.

ADVERTISEMENT

Game da wannan korafin na marubuta maza, na taba tattaunawa da daya daga cikin editocin Sashen Hausa na BBC (na sakaya sunansa), wanda ya shaida mani cewa daya daga cikin manufar gidan rediyon dangane da wannan gasa da ta ta’allaka da mata shi ne, domin su jawo hankalin mata da matasa su rika sauraren tasharsu, domin a bincikensu, sun gano cewa wannan duniyar ta zamani, matasa da mata ne suka fi yawa.

Ta bangaren masu korafi daga masana addinin Musulunci kuwa, wasu sun rika jefa zargi ga BBC Hausa, inda suka ce gidan rediyon ya kirkiro da wannan gasa ga mata zalla da nufin karfafa mata da gurbata su da nufin su rika yin kafada-kafada da maza a matsayin masu ’yanci daya. Ba wannan ma ba kadai, wasu sun zafafa cewa ta hanyar wannan gasa, ana son a sangarta mata su rika gudun kishiya da haihuwar ’ya’ya da yawa da sauransu. Wasu kuma sun nuna cewa ta hanyar wannan gasa, BBC Hausa na yin leken asiri ne, yadda suke tattara bayanai suna kai wa Ingila, domin amfani da su nan gaba domin cin ma wata manufa marar kyau game da al’ummar Hausa da addinin Musulunci.

Ta fuskar masu kishin Adabin Hausa kuwa, wasu sun yi korafin cewa me ya sa BBC Hausa ya zabi nau’in rubutun ZUBE kawai a wannan gasa, alhali akwai sauran nau’ukan rubutu da ya kamata ya fadada? Haka kuma sun kara da cewa, shin me ya sa yau shekara uku da fara wannan gasa, amma BBC bai wallafa littafi ko daya daga dinbin labarun da ya tattara ba? Wasu kuma da suka rika bibiyar gasar, sun yanke hukuncin cewa ba don kishin Hausa aka kirkiro gasar ba, sai don wata manufa boyayya. Masu wannan korafin, sun kafa hujja da cewa, a yayin bikin karrama zakarun gasar, BBC Hausa ba ya amfani da harshen Hausa wajen gudanar da bikin tun daga farko har karshe. Suka ce, ta yaya Sashen Hausa zai shirya gasar rubutun Hausa, ya kira taro amma ya tilasta mutane su rika magana da harshen Ingilishi?

A ganin masu kishin Adabin Hausa, ya kamata BBC Hausa ya rika canja nau’in gasar zuwa WASAN KWAIKWAYO da WAKE, maimakon ZUBE kadai (idan wannan shekarar an yi kan zube, wata shekarar kuma sai a yi kan wake ko wasan kwaikwayo). Masu korafin suka ce kuma ya kamata a rika wallafa fitattu daga cikin labarun da aka tattara zuwa littafi. Ta hanyar littafin, mutane za su samu abin karatu da nazari kuma makarantunmu manya da kanana za su samu abin nazari. Haka kuma sun bayyana cewa ya kamata a yayin taron karrama zakarun gasar, a rika amfani da harshen Hausa, wanda haka zai kara karrama harshen a idon duniya.

Ni dai a ganina, wannan gasa tana da muhimmanci sosai kuma ya kamata Sashen Hausa na BBC ya duba irin korafe-korafen da ke akwai kuma ya duba shawarwarin da ake ba shi, domin ya sake gyara tsarin gasar domin ta dace da kowane tsari kuma domin ta zama mai amfani sosai ga al’umma gaba daya.

Share