✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gasar cin kofin duniya: FIFA ta ba Brazil Dala miliyan 100

Jim kadan da kammala gasar cin kofin zakarun Nahiyoyi da ake fi sani da Confederations Cup a ranar Lahadin da ta gabata, Shugaban Hukumar shirya…

Jim kadan da kammala gasar cin kofin zakarun Nahiyoyi da ake fi sani da Confederations Cup a ranar Lahadin da ta gabata, Shugaban Hukumar shirya wasan kwallon kafa ta duniya (FIFA) Mista Sepp Blatter ya bayyana cewa tuni hukumarsa ta yanke shawarar taimaka wa Brazil da Dala miliyan 100 kwatankwacin Naira biliyan 16 don  ta samu sukunin kammala shirye-shiryen daukar nauyin gasar cin kofin duniya da za a yi a shekara mai zuwa ba tare da matsala ba.
Shugaban ya ce hukumarsa ta yanke wannan shawarar ce bayan la’akari da zanga-zangar da ’yan kasar suka rika yi a lokacin da gasar cin kofin zakarun nahiyoyin ke gudana da aka kammala a karshen makon jiya.  Da yawa daga cikin ’yan kasar nuna bacin ransu ne akan yadda gwamnati ke wandaka da dukiyarsu ne a kan sha’anin wasan kwallo amma ta yi biris da matsalolin da kasar ke ciki na rashin tsaro da rashin abubuwan more rayuwa da kuma rashin aikin yi.
Shugaban ya ce a shekarar 2010 hukumar ta taimakawa Afirka ta Kudu da Dala miliyan 100 bayan ta dauki nauyin gudanar da gasar cin kofin duniya da aka yi a karon farko a Nahiyar Afirka don haka bayar da irin wannan taimako ga Brazil a wannan lokaci ba bakon abu ba ne ga hukumar.
Mista Sepp Blatter ya ce “hukumarsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen taimakawa Brazil a wannan mawuyacin hali da kasar ke ciki musamman yadda ’yan kasar ke neman juya mata baya wajen gudanar da zanga-zangar kin amincewa da neman daukar nauyin gudanar da gasar a shekara mai zuwa.
“Za mu taimaka wa Brazil da Dala miliyan 100 don daukar nauyin gasar cin kofin duniya kuma ina fata hakan zai sanyaya zukatan ’yan kasar”, inji Blatter.
Da yawa daga cikin ’yan kasar sun gudanar da zanga-zangar ce a lokacin da ake gudanar da gasar zakarun Nahiyoyi (Confederations Cup) don nuna adawa da yadda gwamnatin kasar ke kashe biliyoyin Daloli don daukar nauyin gasar cin kofin duniya alhali kasar na fama da matsalar tarbarbarewar tattalin arziki da suka hada da rashin ayyukan yi da rashin tsaro da kuma rashin abubuwan more rayuwa.
Duk da tarzomar da ta gudana, Hukumar FIFA ta yi alwashin ba za ta dauke gasar cin kofin duniya da zai gudana a Brazil a shekara mai zuwa zuwa wata kasa ba.

…Zanga-zanga ta koma ta farin ciki a Brazil

Zanga-zangar da ’yan kasar Brazil suka rika yi a lokacin da gasar cin kofin zakarun Nahiyoyi (Confederations Cup) da aka kammala a ranar Lahadin da ta gabata ta koma ta farin ciki jim kadan bayan Brazil ta lallasa Sifen a wasan karshe da ci 3-0.
Masu zanga-zangar da suka yi dafifi a wajen filin wasa na Maracana a lokacin da ake gudanar da wasan karshe, sun barke da murna ne jim kadan bayan da suka samu labarin kasarsu ce ta samu nasara a wasan karshe da ci 3-0.
Duk da barkonon tsohuwar da jami’an tsaro suka harba don tarwatsa masu zanga-zangar hakan bai hana su shiga sahun sauran ’yan kasar wajen nuna farin cikinsu a kan nasarar da kasar ta samu ba.
Fiye da mutane miliyan daya ne ake sa ran sun shiga cikin zanga-zangar a daukacin kasar tun lokacin da aka fara gasar zuwa karshenta, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya ruwaito.