✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gasar Cin Kofin Duniya Na Matasa A Dubai: Gobe Najeriya za ta kece-raini da Uruguay

A yau Juma’a ne ake sa ran kungiyar kwallon kafa ta Honduras za ta kece raini da ta Sweden yayin da Brazil kuma za ta…

Xan qwallon Najeriya Kelechi Iheanacho a wasan su da Iraqi a gasar cin kofin duniya na matasa da ke gudana yanzu haka a Dubai.  Najeriya ta lallasa Iraqi da ci 5-0 a wasanA yau Juma’a ne ake sa ran kungiyar kwallon kafa ta Honduras za ta kece raini da ta Sweden yayin da Brazil kuma za ta hadu da Medico a wasan kwata fainal a gasar cin kofin duniya na matasa da yanzu haka yake gudana a Dubai.
Haka kuma a gobe Asabar idan Allah Ya kaimu Najeriya za ta hadu da Uruguay sannan Ajantina kuma za ta hadu da ta Kwaddebuwa duk a matakin Kwata-fainal.
A ranar Talatar da ta wuce ne dai Najeriya ta lallasa Iran da ci 4 da 1 a wasa zagaye na biyu da hakan ya sa ta haye zuwa wannan mataki.
Ya zuwa yanzu kasashe takwas ne za su fafata a matakin kwata-fainal don tantance wadanda za su haye zuwa matakin kusa da na karshe watau Semi-Fainal.

… dan Najeriya ya mutu a Dubai bayan ya kalli kwallon Golden Eaglets

Wani abin al’ajabi ya faru a lokacin da wani dan Najeriya da ba a tantance kowane ne ba, ya yanke jiki ya fadi jim kadan da kamala kallon kwallo a tsakanin kungiyar kwallon kafa ta U-17 (Golden Eaglets) da kasar Suwidin (Sweden) a makon  jiya inda aka garzaya da shi asibiti amma kafin wani lokaci rai ya yi halinsa.
Rahotannin da kafar sadarwar naij.com ta kalato ya nuna dan Najeriyar, yana daga cikin magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta ’yan kasa da shekara 17 watau U-17 mai suna Golden Eaglets da yanzu haka take fafatawa a gasar cin kofin duniya da ke gudana a Dubai.
Jim kadan da kallon wasa a tsakanin Najeriya da kasar Suwidin da aka tashi ci uku da uku akan hanyarsu ta komawa Otel din da aka sauke ne al’amarin ya faru bayan an ga mutumin ya yanke jiki ya fadi a cikin motar bas da ke dauke da su inda nan da nan  aka garzaya da shi asibiti mafi kusa don yi masa magani amma kafin a isa rai ya yi halinsa.
Sai dai rahoton da kafar sadarwar ta kalato ya nuna mutumin ya kamu da bugun zuciya ne a lokacin da wasan ke gudana, al;amarin da ya tayar da hankalinsa da kuma na daukacin ’yan kallo a lokacin da wasa ke gudana ganin a farkon rabin lokaci kasar Sweden ce take gaba da ci biyu babu ko daya kafin daga bisani Najeriya ta farke cin da aka yi mata.
Wani abokin mamacin da bai so a ambaci sunansa ba, ya tabbatar da uakuwar lamarin.
“Na lura a lokacin da wasa ya yi zafri, hakalin abokina ya tashi, ya soma wadansu dabi’u da ban gane ba, ana tashi wasan muna tafiya a cikin mota kwatsam sai muka ga ya yanke jiki ya fadi sumamma amma kafin a garzaya da shi asibiti rai ya yi halinsa”, inji abokinsa a lokaicn da yake juyayin al’amarin.
Ya zuwa lokacin buga wannan labari, duk kokarin da manema labarai suka yi don jin ta bakin mahukuntan asibitin da suka kwantar da dan Najeriyar, abin ya ci tura.  Haka ma ba a samu takamaiman bayani daga wajen mahukunta  Najeriya ba.