✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gasar Cin Kofin Duniya Na Matasa A Dubai: Yau Najeriya za ta yi wasan karshe da Meziko

A yau Juma’a ne ake sa ran kungiyar kwallon kafa ta ’yan kasa da shekara 17 (U-17) da ake wa lakabi da Golden Eaglets za…

A yau Juma’a ne ake sa ran kungiyar kwallon kafa ta ’yan kasa da shekara 17 (U-17) da ake wa lakabi da Golden Eaglets za ta kece-raini da Meziko a wasan karshe na gasar cin kofin duniya na matasa da ke gudana a Dubai.

A ranar Talatar da ta wuce ne dai kungiyar kwallon kafa ta Golden Eaglets ta fitar da Sweden da ci 3-0 da hakan ya ba ta damar zuwa wasan karshe.
A bangaren Meziko kuwa, kasar ta lallasa ta Ajantina ce ita ma da ci 3-0 da hakan ya sa ta kai wasan karshen.
Sai dai a wasan da kasashen Najeriya da Meziko suka yi a wasansu na farko, Najeriya ce ta lalllasa Meziko da ci 6-1.
A wannan karo, daya daga cikin zaratan ’yan kwallon Meziko mai suna Iban Ochoa da ya zura kwallaye biyu daga cikin ukun da suka doke Ajantina a ranar Talatar da ta wuce ya ce kasar ta sha alwashin rama cin da Najeriya ta yi mata a yau.
Ya ce ’yan wasan Meziko za su yi amfani da wannan dama don ganin sun rama cin da Najeriya ta yi musu a kwanakin baya.
“Abin da za mu yi mu huce haushin cin da Najeriya ta yi mana a baya shi ne mu lashe kofin duniya na matasa a yau”, inji shi.
Sai dai kocin Najeriya Manu Garba ya ja hankalin ’yan wasansa da su zage damtse don ganin sun lashe kofin. Ya ce kada su kuskura su ce don sun samu galaba a kan Meziko a wasansu na farko da ci 6-1 a wannan lokaci ma haka abin zai kasance.
Kocin ya hore su da su yi kokari da kuma yin taka-tsan-tsan don ganin sun kare martabar kasar nan da ma yankin Afirka a idon duniya ta hanyar lashe kofin.
A halin yanzu Najeriya na neman kafa tarihi idan ta lashe kofin don za ta lashe sau hudu kenan a tarihin gasar. Ya zuwa wannan lokaci babu kasar da ta taba lashe kofin har sau hudu.
A bangaren Meziko kuma, tana neman kafa tarihin kasar da ta lashe kofin sau biyu a jere a tarihin gasar.
Yanzu dai duniya ta zuba ido ta ga yadda wasan zai kasance don tantance kasar da za ta lashe kofin.