✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gasar cin kofin kalubale na Nahiyoyi: ’Yan Brazil sun cigaba da yin zanga-zanga

Zanga-zanga ta cigaba da gudana a lokacin da gasar cin kofin kalubale na Nahiyoyi da aka fi sani da Confederation Cup ke gudana a halin…

Zanga-zanga ta cigaba da gudana a lokacin da gasar cin kofin kalubale na Nahiyoyi da aka fi sani da Confederation Cup ke gudana a halin yanzu a kasar Brazil.
Rahotanni da ke fitowa sun ce tun a ranar da aka fara gasar ce watau a ranar Asabar ta makon jiya, wasu ’yan kasar Brazil su kimanin dubu daya suka mamaye filin kwallon da aka fara gudanar da gasar inda suka rika rera-wakokin tofin Allah-tsine ga gwamnatin kasar wajen kashe makudan kudi don daukar nauyin gasar cin kofin duniya da zai gudana a kasar a shekara mai zuwa alhali kasar na fuskantar tabrbarewar tattalin arziki.
Masu zanga-zangar sun zargi gwamnatin ce da yin baki biyu wajen kashe kudinsu ba tare da amincewarsu ba a shirye-shiryen da kasar ke yi na daukar nauyin gasar cin kofin duniya da zai gudana a shekara mai zuwa.
Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya ruwaito zanga-zangar ta gudana ne a lokacin da wasa ke gudana a tsakanin Brazil da Japan a wasan farko sannan a washegari ake sake gudanar da irinta a lokacin wasa a tsakanin kasashen Meziko da Italiya a filin wasa na Maracana inda fiye da mutum dubu suka yi arangama da jami’an tsaro kuma aka jikkata wasu da dama.
Rahoton ya ce jami’an tsaron sun yi amfani da harsashin roba da kuma barkonon tsohuwa ne wajen tarwatsa masu zanga-zangar da hakan ta janyo da dama suka jikkata sai dai ba a samu wani rahoton rasa rai ba.
Tuni gwamnatin kasar ta fitar da sanarwar haramta yin zanga-zanga a lokacin da gasar ke gudana.  Gwamnatin ta ce za ta sanya kafar wando daya ga duk wanda ya nemi kawo cikas a yayin da gasar ke gudana.
Su dai ’yan kasar suna zargin gwamnati ce da yin baki biyu inda ta nuna ba za ta yi amfani da dukiyar kasar wajen daukar nauyin gasar cin kofin duniya da zai gudana a shekara mai zuwa ba amma sai aka samu akasin haka.
’Yan kasar sun gano cewa gwmanati ta dukufa wajen kashe dukiyarsu ce a harkar kwallo a yayin da suke fuskantar tsadar rayuwa.
Wani rahoto ya ce ya zuwa yanzu kasar ta kashe akalla Fam miliyan 358 wajen gina filin wasa daya da za a yi amfani da shi a lokacin gasar cin kofin duniya.
Sai dai ana sa ran gwamnati ta shawo kan al’amarin zanga-zangar ya zuwa shekaranjiya Laraba.
Najeriya tana daya daga cikin kasashe takwas da suka halarci gasar da ke gudana a halin yanzu.
A jiya Alhamis kungiyar kwallon kafa ta Najeriya da aka fi sani da Super Eagkes ce ta kece-raini da kasar Uruguay a wasa na biyu.