✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gasar cin kofin zakarun Nahiyoyi: barayi sun yi wa ’yan kwallon Sifen lalata

Jami’an tsaron kasar Brazil sun dukufa  wajen zakulo barayin da suka shiga dakunan kwanan ’yan kwallon Sifen a Otal din da aka sauke su inda…

Jami’an tsaron kasar Brazil sun dukufa  wajen zakulo barayin da suka shiga dakunan kwanan ’yan kwallon Sifen a Otal din da aka sauke su inda suka wawushe musu kudi da kadarorin da ya zuwa wannan lokaci ba a tantance yawansu ba.
A lokacin da al’amarin ya faru, an ce ‘yan kwallon sun tafi filin wasa ne don kara wa da kasar Uruguay a ranar Litinin ta makon jiya a gasar cin kofin kalubale na Nahiyoyi da ake wa lakabi da Confederations Cup da yanzu haka yake gudana a Brazil.  Bayan an tashi daga wasan ne jim kadan da komawa masaukinsu, shida daga cikin ’yan kwallon da suka hada da Gerard Pikue suka sanar da jami’ansu abin da ya faru na wawushe musu dukiya da kuma kadarorinsu.  Nan da nan su kuma jami’an nasu suka sanar da ’yan sandan yankin halin da ake ciki.
Jaridar Marca ta Sifen ta ce ’yan wasan sun gabatar da kokensu ga jami’ansu ne inda su kuma suka mika koke ga jami’an tsaro na ’yan sandan yankin da su kuma suka bazama don kamo wadanda suka aikata  wannan ta’asa.
Sai dai a lokacin da aka tuntubi jamii’in hulda da ’yan jaridu na kulob din ya ki yin sharhi a kan batun.  Haka kuma duk kokarin da aka yi na tuntubar jami’n tsaron da ke kula da yankin Recife da ke Brazil don jin ta-bakinsa a kan al’amarin abin ya faskara.
Brazil dai ta yi kaurin suna wajen aikata miyagun laifuka da suka hada da fashi da makami da sata.