Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Gasar damben gargajiya a Zariya tana kayatarwa

A ranar Lahadin da ta gabata ce ’yan wasan damben gargajiya suka cika makil a Zariya domin ci gaba da fafata wasan damben da ake yi a kowane yamma a filin wasan kwallon kafa da ke Layin Club Street a Karamar Hukumar Sabon Gari a Jihar Kaduna.

Filin dambe ya cika da ’yan kallo da bakin shahararrun ’yan wasan dambe gargajiya daga sassan kasar nan da suka fito daga bagarorin Gurumada da  Arewa da  kuma Kudu.

ADVERTISEMENT

’Yan wasan sun fito ne daga jihohin Sakkwato da Zamfara da Kebbi da Kano da kuma Jigawa.

Manyan ’yan wasa ne suka fafata a wasanni daban daban, inda a wasa na farko aka gwabza  a tsakanin Dan Libanda da Autan Fafa ba tare da kisa ba.

ADVERTISEMENT

Wasa na biyu an yi ne a tsakanin Kurumure na Dogon Auta da Dan Yalo Shagon Jamilu, inda Kurumure na Dogon Auta ya kashe Dan Yalo Shagon Jamilu a zagaye na biyu.

Sai wasa na uku wanda shi ne ya fi jan hankali tare da kayatarwa an kece-raini ne a tsakanin Maitakwasara daga Gurumada da Mai Maciji daga bangaren Kudu, inda Maitakwasara ya kashe Mai Maciji a zagaye na uku.

Bayan kammala fafatawar ce Aminiya ta ji ta bakin wanda ya yi kisan wanda ya ce:  “Sunana Abubakar Umar wanda aka fi sani da Maitakwasara kuma ni mutumin Birnin Kebbi ne kuma dambe gadonsa na yi tun daga kakana har zuwa ga iyaye, kuma tun ina dan shekara takwas na fara dambe. Kuma na samu dimbin nasarori a harkar don na dauki dambe a matsayin sana’a wadda na yi gado, don haka ba na wasa da harkar.  Fatata a wannan harka ita ce yadda na shigo lafiya Allah Ya sa in fita lafiya.”

Aminiya ta ji ta bakin alkalin wasa mai suna Shamsu wanda aka fi sani da A-Kashe inda ya yi karin bayani kamar haka:  “Harkar dambe tana tafiya a garin Zariya domin muna da shahararrun ’yan wasa daga sassan kasar nan da suke halartar wannan wasa.  Kuma daga ganin yadda wasannin suke gudana ka san harkar wasan damben gargajiya tana kankama a Zariya, domin kullum sai bunkasa take yi.  Sai dai akwai abin da muke kira tare-wawa a harkar dambe, wato a kai wa dan dambe dauki idan yana neman faduwa bayan an naushe shi musamman a wasan da ya gudana a tsakanin Kurumure da Yalo amma in ban da wasan, babu inda aka samu haka.

Sarkin Makadan ’Dambe, Dan Moyi da jama’arsa daga Jihar Sakkwato sun nishadantar da filin wasan da kade-kade da bushe-bushe kamar yadda aka saba.