✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gasar Firimiya:  Gobe Arsenal za ta shawo ta da Tottenham

A ci gaba da fafatawa a gasar rukuni-rukuni na Ingila da aka fi sani da Firimiya, gobe Asabar ne za a yi karon battar a tsakanin…

A ci gaba da fafatawa a gasar rukuni-rukuni na Ingila da aka fi sani da Firimiya, gobe Asabar ne za a yi karon battar a tsakanin kulob din Arsenal da Tottenham.

Wasan zai gudana ne a filin wasan Arsenal na Emirates da misalin karfe 1:30 na rana agogon Najeriya.

Ana sa ran wasan zai kayatar ganin yadda kungiyoyin biyu ke fafutikar gamawa a sahun farko a teburin gasar da hakan zai ba su damar hayewa zuwa  gasar cin Kofin Zakarun Kulob na Turai.

A shekaranjiya Laraba ce kulob din Arsenal ya lallasa na Bournemouth da ci 5-1 yayin da kulob din Tottenham ya sha kashi a wajen Chelsea da ci 2-0.

Kawo yanzu kulob din Liberpool ne yake jan ragamar gasar da maki 69 sai na Manchester City da ke biye da maki 68 sai Tottenham da maki 60 sai Arsenal a matsayin ta hudu da maki 56.