✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gasar Firimiya: Gobe za a shawo ta tsakanin Man City da Chelsea

A ci gaba da fafatawa a gasar rukuni-rukuni ta Ingilia da aka fi sani da gasar Firimiya, a gobe Asabar za a yi wasa mafi zafi…

A ci gaba da fafatawa a gasar rukuni-rukuni ta Ingilia da aka fi sani da gasar Firimiya, a gobe Asabar za a yi wasa mafi zafi a wannan mako.

Wasan karo na 13 za a yi ne tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Manchester City da ta Chelsea a filin wasa na City da ake kira Etihad Stadium da misalin karfe biyar da rabi na yamma agogon Najeriya.

Wasan zai yi zafi ganin kawo yanzu Man City tana matsayi na 4 a teburin gasar.

A wasa karo na 12 ne kulob din Liberpool ya lallasa City da ci 3-1 al’amarin da ya sa City ta koma matsayi na 4 daga matsayi na 2.

Manchester City ce take rike da kofin bayan ta lashe sau biyu a jere, sai dai a bana tana fuskantar kalubale a gasar.

Kawo yanzu Liberpool ce take jan ragamar gasar bayan ta hada maki 34 a wasa 12 sai kulob din Leicester City ke biye da maki 26, Chelsea ma ta hada maki 26 ne amma saboda bambancin kwallaye ya sa ta kasance ta uku sai kulob din Man City ke matsayi na 4 da maki 25.

Ke nan idan City ta yi kunnen doki ko ta samu rashin nasara a wasan na gobe, to za ta sake yin kasa a teburin gasar kamar yadda jadawalin gasar ya nuna.

Masoya kwallon kafa musamman magoya bayan kungiyoyin biyu sun zuba ido su ga yadda wasan na gobe zai kaya.