Daily Trust Aminiya - Gasar Firimiya: Gobe za a shawo ta tsakanin Tottenham da Lib
Subscribe

Gasar Firimiya: Gobe za a shawo ta tsakanin Tottenham da Liberpool

A ci gaba da fafatawa a gasar Firimiya ta Ingila mako na 22 a gobe Asabar idan Allah Ya kai mu za a yi wasa mai zafi a tsakanin kulob din Tottenham da na Liberpool a filin wasa na Tottenham da misalin karfe 6:30 na yamma agogon Najeriya a wasan da ake jin shi ne mafi zafi a wannan mako.

Kawo yanzu Liberpool ce take jan ragamar gasar da maki 58 a wasa 21 kuma tana da kwantan wasa daya da West Ham United.  Sannan kawo yanzu ba ta samu rashin nasara a wasa ko daya ba in ban da kunnen doki da ta yi da kulob din Manchester United.

A bangaren Tottenham kuwa, ita ce ta 6 a jerin kungiyoyin da ke fafatawa a gasar bayan ta hada maki 30 a wasa 21.

A zagayen farko Liberpool ce ta lallasa Tottenham da ci 2-1 al’amarin da ya sa sabon kocin Tottenham, Jose Mourinho yake kokarin ganin ya doke Liberpool a wannan karo don ya taka mata birki.

texem
More Stories