Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Gasar Firimiya:  Jibi za a gwabza tsakanin Tottenham da Man United

A ci gaba da fafatawa a gasar rukunn Firimiya ta Ingila a jibi Lahadi ne ake sa ran gwabza wasa mai zafi a tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Tottenham da ta Manchester United.

Kawo yanzu kulob din Tottenham ne na uku a teburin gasar yayin Manchestar United ke matsayi na 6.

ADVERTISEMENT

Ganin yadda kulob din Man United yake tashe bayan da ya yi sabon koci, Ole Gunnar Soljskjear ya sa ake ganin wasan zai yi zafi.  A wasa zagayen farko Tottenham ce ta bi United har gida ta lallasa ta da ci 3-0.

Masana harkar kwallo suna ganin wannan shi ne wasa mafi zafi da kulob din United zai fuskanta bayan da ya yi sabon koci, inda kawo yanzu United ta lashe wasa 4 a jere bayan zuwansa.

ADVERTISEMENT

Idan Tottenham ta samu nasara a wasan, to za ta karya lagon United, yayin da idan United ce ta samu nasara, za ta ci gaba da haskakawa a gasar.

Wasan zai gudana ne da misalin karfe 5:30 na yamma agogon Najeriya kuma ana sa ran gidajen kallon kwallo za su cika makil da masoya kwallon kafa musamman magoya bayan kungiyoyin kwallon kafar biyu.