✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gasar Firimiya: Jibi za a shawo ta tsakanin Man Utd da Chelsea

A jibi Lahadi ne ake sa ran za a yi wasa mai zafi a gasar Firimiya ta Ingila inda za a shawo ta a tsakanin Manchester…

A jibi Lahadi ne ake sa ran za a yi wasa mai zafi a gasar Firimiya ta Ingila inda za a shawo ta a tsakanin Manchester United da kuma kulob din Chelsea.

Za a yi wasan ne a filin wasa na OId Trafford, wato gidan United da misalin karfe 4:30 na yamma agogon Najeriya.

Wasan zai yi zafi ne ganin dukkan kungiyoyin biyu suna fafutikar ganin sun gama a kungiyoyi hudu da ke saman teburin gasar a karshen kakar wasa ta bana.

Bayan wannan  wasa, zai kasance saura wasanni biyu a kammala gasar ta bana ke nan.

Kawo yanzu kulob din Manchester City ne yake saman teburin gasar da maki 89 sai kulob din Liberpool ke biye da maki 88 sai Tottenham da ke biye da maki 70 sai Chelsea da ke matsayin na hudu da maki 67 sai kulob din Arsenal a matsayi na biyar da maki 66 sai kulob din Man United da ke matsayi na 6 da maki 64.

Wasan na jibi za a hadu ne a tsakanin Chelsea da ke matsayi na 4 da Man United da ke matsayi na 6. Duk kungiyar da ta yi sake aka doke ta za a yi mata sakiyar da babu ruwa, don za a yi mata nisa ke nan.

Idan United ta yi sake aka doke ta, za ta shiga halin ni-’ya-su domin da wuya ne in za ta iya gamawa a kungiyoyi hudun da za su kasance a saman teburin gasar a kakar wasa ta bana.

Haka abin yake ga kulob din Chelsea, shi ma idan ya sake aka doke shi, to zai iya fadawa cikin matsala.

Masoya kwallon kafa dai sun zuba ido su ga yadda wannan wasa zai kaya.