Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Gasar Firimiya: Jibi za a yi gumurzu tsakanin Arsenal da Tottenham

A jibi Lahadi ce za a fafata wasa mai zafi a tsakanin kulob din Arsenal da na Tottenham a gasar rukuni-rukuni na Ingila na Firimiya.

Wasan zai gudana ne da misalin karfe 3:05 na rana agogon Najeriya, kuma ana sa ran masoya kwallon kafa za su kashe kwarkwatar ido don ganin yadda wannan wasa mai zafi zai kaya.

ADVERTISEMENT

Kawo yanzu kulob din Manchester City ne ke saman teburin gasar da maki 35 bayan an yi wasanni 13.  Sai Liberpool a matsayi na biyu da maki 33 sai Tottenham da ke matsayi na uku da maki 30 sai Chelsea a matsayi na 4 da maki 28 sai kulob din Arsenal a matsayi na 5 da maki 27.

Dukan kungiyoyin biyu suna tashe a gasar ta bana, musamman idan aka lura da yadda kulob din Tottenham ya lallasa na Chelsea da ci 3-1 a karshen makon jiya.  Ita kuwa Arsenal sau biyu kacal aka doke ta tun bayan da aka  fara gasar ta bana, wanda hakan ya sa ta yi wasanni fiye da 10 ba tare da an samu nasara a kanta ba.

ADVERTISEMENT