✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gasar Firimiya: Jibi za a yi karon batta tsakanin Manchester City da Manchester Utd

A ci gaba da fafatawa a gasar rukuni-rukuni na firimiyar Ingila, a jibi Lahadi idan Allah Ya kai mu za a yi wasa mai zafi…

A ci gaba da fafatawa a gasar rukuni-rukuni na firimiyar Ingila, a jibi Lahadi idan Allah Ya kai mu za a yi wasa mai zafi a tsakanin manyan kulob biyu.

Kulob din da za su hadu don yin wannan wasa su ne na Manchester City da kuma na Manchester United.

Za a yi wasan ne a filin wasan kulob din Man City da misalin karfe 4:30 na yamma agogon Najeriya.

Masoya kwallon kafa suna yi wa wadannan kulob biyu lakabi ne da Manchester birni (City) da kuma Manchester kauye (United), ganin sun fito ne daga gari daya a Ingila.

Kawo yanzu kulob din Manchester City ne yake saman teburin gasar da maki 29 bayan an yi wasanni 11.  Sannan kulob din sau biyu kacal ya yi kunnen doki tun bayan da aka fara gasar da hakan ta sa ya dare teburin gasar.  Kenan Manchester City ta yi wasanni 11, inda ta yi kunnen doki 2 kuma ta samu nasara a wasanni 9 inda ta hada maki 29.

A bangaren Manchester United kuwa, kawo yanzu ita ce ta 7 a teburin gasar, bayan ta yi wasanni 11, ta yi kunnen doki a wasanni biyu, sannan ta samu rashin nasara a wasanni uku, yayin da ta samu nasara a wasanni shida, inda ta hada maki 20.

Idan City ce ta samu nasara a wannan wasa, za ta ci gaba da jan ragamar gasar, yayin da idan United ce ta doke City za ta farfado da martabarta a gasar.

Kamar kullum, ana sa ran gidajen kallon kwallo za su cika makil daga wajen masoya kwallon kafa don ganin yadda wannan wasa zai kaya.

Fatarmu dai kamar kullum a yi kallo lafiya, kuma a tashi lafiya.