Da Dumi Dumi

Gasar Kofin Duniya na ’Yan shakara 17: Najeriya ta tsallake zuwa zagaye na biyu

Ibrahim Sa’id dan wasan Kungiyar Golden Eaglets ta Najeriya
Ibrahim Sa’id dan wasan Kungiyar Golden Eaglets ta Najeriya

Kungiyar kwallon kafa ta ’yan kasa da shekara 17 Golden Eaglets ta samu nasarar  hayewa zuwa zagaye na biyu bayan da ta lallasa kasar Ecuador da ci 3-2.

Tun farko Ecuador ta fara zura wa Najeriya kwallaye biyu a raga kafin daga bisani labari ya canja bayan an dawo daga hutun rabin lokacin inda Kocin ’yan Najeriya Manu Garba ya shigo da wani hazikin dan wasa Ibrahim Sa’id wanda ya zura kwallaye uku a ragar kasar Ecuador kuma hakan ya ba Najeriya damar wucewa wasan zagaye na gaba.

Tun a makon jiya ne Shugaba Muhammadu Buhari ya ce zai ci gaba da bin wasannin da kungiyar ta Golden Eaglets ke yi sau-da-kafa, a gasar da kasar Brazil ke karbar bakunci.

Shugaba Buhari ya bayyana jin dadinsa game da nasarar da Golden Eaglets ta samu a wasan da ta ci kasar Hungary 4-2 a daren Asabar da ta gabata.

“Wasanmu na farko a Brazil ya yi kyau matuka kuma ya sa ni alfahari,” Buhari ya wallafa a Twitter.

ADVERTISEMENT

Matasan Najeriya ne suka lallasa na kasar Hungary a wasan da aka zura kwallo har shida.

Gyorgy Komaromi na Hungary ne ya fara saka kasarsa a gaba minti 3 da fara wasa kafin Samson Tijani ya farke wa Najeriya daga bugun finareti.

Hungary ta kara kwallo ta biyu ta hannun Samuel Major a minti na 28, inda Usman Ibrahim ya farke a minti na 79.

A minti goman karshe na wasan ne ’yan wasan Najeriya suka zura kwallo biyu ta hannun Oluwatimilehin Adeniyi da Samson Tijani.

Wannan nasara ta sa Shugaba Buhari ya ce da ma ya san za a rina: “Na tabbata sun shirya tsaf domin lashe kofin a karo na shida.

“Tun lokacin da suka isa Brazil nake biye da su kuma na lura da irin himma da kwarin gwiwarsu. Wannan shi ne abin da aka san ’yan Najeriya da shi.

Ni da kaina zan ci gaba da bibiyar wasanninsu a wannan gasar,” inji Shugaba Buhari,

A tarihin gasar, Najeriya ce ta fi lashe kofin inda ta lashe gasar har sau biyar a 1985 da 1989 da 1993 da 2007 da 2013 da kuma 2015 baya ga karewa a mataki na biyu da ta yi sau uku.

Najeriya tana rukuni na B ne tare da Hungary da Ecuador da Austireliya. Matasan za su yi wasan karshe a matakin rukuni da Australia a yau Juma’a 1 ga Nuwamba.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya