✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gasar Kwallon Kafa ta Wilson Ilya ta kankama

An fara gasar wasan kwallon kafa na tsohon dan takarar Majalisar Dokokin Jihar Kaduna daga Karamar Hukumar Jama’a a karkashin Jam’iyyar APC, Wilson Iliya a…

An fara gasar wasan kwallon kafa na tsohon dan takarar Majalisar Dokokin Jihar Kaduna daga Karamar Hukumar Jama’a a karkashin Jam’iyyar APC, Wilson Iliya a garin Jagindi Tasha da ke Karamar Hukumar Jama’a a Jihar Kaduna.

Yayin da yake jawabi wajen bude gasar, tsohon Dan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar Sanga da Jama’a , Mista Boniface Garba ya ce wannan shi ne kashi na farko na gasar da suke sa ran za ta kewaye dukkan shiyyoyi uku na karamar hukumar kafin a buga wasan karshe a tsakanin kananan hukumomin biyu.

Wanda ya dauki nauyin shirya gasar, Wilson Ilya ya ce tunanin hakan ya biyo bayan alkawuran da ya yi ne a lokacin zaben 2019 da ya gabata na tallafa wa matasa ta hanyar wasanni da fannin ilimi da kuma sana’a.

An sanya kyautar Naira dubu 100 da kayan wasa da suka hada da riguna da wanduna da takalman kwallo ga kungiyar da ta zo ta daya, yayin da ta biyu da ta uku za su samu kyautar Naira dubu 50 da dubu 25 bi-da-bi da kuma kayayyakin wasan kwallo.

Wasan, wanda ake sa ran kammalawa a ranar 11 Afrilu, an bude ne da wasa a tsakanin kungiyoyin kwallon kafa na Unguwar Sanda da Ghauta, inda Unguwar Sanda ta doke takwararta ta Ghauta da ci 3-0.