✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gasar Neman Zuwa Cin Kofin Duniya A Brazil: An hada Super Eagles da Etofiya

A ranar Litinin da ta gabata ne Hukumar kula da shirya kwallo a Nahiyar Afirka (CAF) ta fitar da jadawalin kasashe goma da za su…

kocin Super Eagles Stephen KeshiA ranar Litinin da ta gabata ne Hukumar kula da shirya kwallo a Nahiyar Afirka (CAF) ta fitar da jadawalin kasashe goma da za su hadu da juna a gasar neman hayewa zuwa cin kofin duniya da zai gudana a Brazil a shekara mai zuwa.
kasashe goma da suka hada da Najertiya da Aljeriya da Burkina Faso da Kamaru da Kwaddebuwa, da Masar da Etopiya da Ghana da Senegal da kuma Tunisiya ne aka hada su don tantance biyar daga ciki wadanda za su yi wasa a tsakaninsu gida da waje don samun biyar din da za su haye zuwa gasar.
An hada Najeriya ne da Etopiya kamar yadda aka ambata a baya yayin da aka hada Kwaddebuwa da Senegal.  Tunisiya za ta kece-raini ne da Kamaru yayin da Ghana kuma za ta kara da Masar sai Burkina Faso kuma ta hadu da Aljeriya.
Ana sa ran a buga wasan farko ne a tsakanin ranakun 11 zuwa 15 ga watan Oktoba, 2013 yayin da za a buga wasanni na biyu a tsakanin ranakun 15 zuwa 19 ga Nuwamban 2013.
Duk kasashe biyar din da suka samu nasara su za su wakilci Afirka a gasar cin kofin duniya da zai gudana a Brazil a shekara mai zuwa idan Allah Ya kaimu.