✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gasar Oscar: An cire fim din Najeriya na farko da ya shiga gasar saboda Ingilishi

Tun a watan jiya ne masu kallon fina-finai da masu ruwa-da-tsaki a harkar suke murna ganin cewa fim din Najeriya na farko ya samu shiga…

Tun a watan jiya ne masu kallon fina-finai da masu ruwa-da-tsaki a harkar suke murna ganin cewa fim din Najeriya na farko ya samu shiga cikin faina-finan da za su fafata a gasar fim ta duniya da ake kira Oscar Award.

Kwatsam sai murna ta koma ciki, bayan da Kwalejin da ke kura da gasar. Wato The Academy of Motion Picture Arts and Sciences ta sanar da cire fim din mai suna Lionheart, saboda an fi yin amfani da Turancin Ingilishi.

Fim wanda sananniyar ’yan fim ta Kudancin Najeriya Genebiebe Nnaji ta dauki nauyi, kuma ta bada umarni, da farko ya shiga cikin fina-finai 92 na duniya, amma a ranar Litinin da ta gabata sai aka sanar da cire shi.

A ka’ida, duk fim din da zai shiga wannan rukunin na gasar ta Oscar, dole ya zama ba na Amurka ba ne, kuma ba a can aka dauke shi ba, sannan ya kasance ba da Ingilishi aka yi ba, amma ba laifi a dan jefa Ingilishin a ciki.

Amma shi fim din Lionheart da Ingilishi aka yi shi, minti 12 kawai aka yi da harshen Ibo a fim din, wanda hakan ya sa aka cire shi kasancewar Turancin ya fi yawa.

Fim din ya nuna wata mata mai suna Adaeze, wadda ita da kanta Genebiebe ta hau matsayin ke kokarin tafiyar kasuwancin gidansu na harkokin sufuri, da wahalar da ta sha sauransu.

Genebiebe ta bayyana takaicinta kan lamarin, inda ta ce dole a yi amfani da Ingilishi a fim din Najeriya kasancewar shi ne harshen da ake amfani da shi, “Ni ce darakta a fim din Lionheart, kuma mun yi amfani da harshen da muke amfani da shi ne a Najeriya. Ingilishi ne harshen da ke hada kan harsunan Najeriya sama da 500 da ake amfani da su a Najeriya, wanda hakan ya sa muka zama kasa daya.”