✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gasar Rubutun Afrika Ta Caine: ’Yan Najeriya sun yi zarra

A Gasar Rubutun Afrika Ta Caine ta bana, zaratan marubuta kirkirarrun labarai daga Najeriya ne suka yi zarra a fadin duniya. Cikin marubuta biyar da…

Zaratan zakarun Afrika, daga hagu, Elnathan John, Abubakar Adam Ibrahim, Chinelo Okparanta, Tope Folarin da kuma Pede Hollist  A Gasar Rubutun Afrika Ta Caine ta bana, zaratan marubuta kirkirarrun labarai daga Najeriya ne suka yi zarra a fadin duniya. Cikin marubuta biyar da suka tsallake shingen sauran marubutan duniyar Afrika da suka fafata a gasar, mutum hudu duk ’yan Najeriya ne, a yayin da mutum daya ya fito daga kasar Saliyo.
A yayin da ya ambata sakamakon gasar a maraicen Litinin da ta gabata a harabar dakin karatu na Bodleian da ke Odford, Ingila, shugaban tawagar alkalan da suka yi alkalanci a gasar, Gus Casely-Hayford, ya bayyana sunan dan Najeriya Tope Folarin a matsayin wanda ya zama zakara da labarinsa mai taken ‘Miracle’ (Al’ajabi).
kirkirarren gajeren labarin ‘Miracle,’ an kitsa shi bisa labarin yadda wani fasto ya yi wa makaho addu’a kuma ya warke, ya samu idanuwansa biyu suka dawo garau. Gus Casely ya bayyana labarin da cewa ya tsaru kuma ya cancanci ya zama zakara a wannan gasa ta bana.
Game da zakaran na bana kuwa, Tope Folarin dan Najeriya ne da ya yi karatunsa Morehouse College da Jami’ar Odford, inda ya samu digiri har biyu. A yanzu haka yana aiki ne a birnin Washington, Amurka.
Shi kuwa marubuci Pede Hollist, shi ya zama mai take wa zakaran baya, ya zo na biyu a gasar da labarinsa mai taken ‘Foreign Aid’ (Tallafin kasashen ketare). Shi mutumin kasar Saliyo ne amma yana koyar da Ingilishi a Jami’ar Tampa da ke birnin Florida, Amurka. Kafin ya samu wannan nasara a fagen rubutu, ya rubuta littattafai da dama, wadanda suka hada da ‘Going to America’ da sauransu.
Alkalin gasar ya ambata sunan marubuci Abubakar Adam Ibrahim, a matsayin wanda ya zo na uku a gasar, da labarinsa mai taken ‘The Whispering Trees’ (Bishiyoyi Masu Rada). An tsamo labarin ne daga littafinsa na gajerun kirkirarrun labarai, mai taken labarin, wanda kamfanin Parrésia Publishers da ke Legas-Najeriya ya wallafa.
Abubakar ya kasance dan asalin garin Jos, Jihar Filato. dan jarida ne shi da ke aiki a kamfanin Media Trust Limited Abuja Najeriya, masu wallafa jaridun Daily Trust, Weekly Trust, Sunday Trust da Aminiya. Shi ne Editan Adabi na jaridar Sunday Trust, wacce ke fitowa duk kowace Lahadi. Kafin ya samu wannan nasara a bana, ya taba cin gasar rubutu ta BBC a 2007, mai taken ‘BBC African Performance Prize.’
Marubucin da ya zo na hudu a wannan gasa ta Caine, shi ne Elnathan John. Ya samu nasara ne da labarinsa mai taken ‘Bayan Layi.’
Shi ma dan Najeriya ne daga garin Zonkwa, Jihar Kaduna. Ya yi karatunsa na Lauya a Jami’ar Ahmadu Bello Zariya. Sai dai maimakon ya ci gaba da aiki a bangarensa da ya kware na Lauya, sai ya zabi ya kasance marubuci, wanda a yanzu haka yana daya daga cikin masu rubutu na musamman a jaridar Sunday Trust.
Chinelo Okparanta, ’yar asalin Fatakwal Najeriya, mace daya tal cikin zakarun gasar, ita ce ta zo ta biyar da labarinta mai taken ‘America’ (Amurka). Ta yi rubuce-rubuce da dama na kirkirarrun labarai, a yanzu haka tana aikin koyarwa ne a Jami’ar Colgate da ke Amurka.
Kamar yadda ka’idar gasar ta tanada, zakaran da ya zo na daya, zai amshi kyautar Fam 10, 000, sannnan kuma zai samu damar zaman bakunci na tsawon wata daya cur a mazaunin marubuta na Jami’ar Georgetown.
A tarihin gasar, a bara ma dan Najeriya Rotimi Babatunde ne ya zama zakara. A 2000, marubuciya ’yar Sudan Leila Aboulela ce ta cinye. A 2001 kuma wani dan Najeriya, Helon Habila ya zama zakara.
Game da wannan gasa ta Caine, an fara gudanar da ita ne a 2000, yayin gudanar da Kalankuwar Littattafai Ta Duniya da aka gudanar a Harare, Zimbabwe. An yi mata lakabi ne daga sunan Sir Michael Caine, wanda kafin mutuwarsa, shi ne Shugaban Kamfanin Booker Plc, mai wallafa littattafai. Shi ne kuma ya taba jagorantar Kalankuwar Marubutan Afrika mai taken ‘Africa 95’ da aka gudanar a Nahiyar Turai da Afrika.
Kafin mutuwarsa Michael Caine yana kan shiri da tunanin yadda zai fito da hanyoyin bunkasa harkar rubuce-rubuce a Afrika, musamman ta bangaren rubutu da Ingilishi, amma bai samu kammala shirinsa ba rai ya yi halinsa. Dalili ke nan abokansa suka kafa gidauniyar tunawa da shi, suka ware Fam 10,000 domin gudanar da wannan gasa a duk shekara.